“Allah mun tuba, mu na da-na-sanin zaɓen Buhari” -Oyinlola, Tsohon Gwamnan Osun

Tsohon Gwamnan Osun, Olagunsoye Oyinlola ya nemi gafarar Ubangiji bisa abin da ya kira “zurɓabiyar rashin sanin” da ta kwashe su har su ka zaɓi Shugaba Muhammadu Buhari.

Oyinlola ya yi wannan kakkausar su ka ne saboda da yadda ya ce su ka riƙa yabon iya sallar Buhari wajen tunanin zai iya magance matsalar tsaro, amma sai ga shi ko alwala bai iya ba

Oyinlola wanda ya yi Gwamnan Osun daga 2003 zuwa 2010 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, daga baya ya koma APC kafin zaɓen Gwamna a 2014.

Ya na daga cikin waɗanda su ka riƙa yi wa Buhari kamfen wurjanjan kafin zaɓen 2015.

Da ya ke magana a Sashen Yarabanci na BBC a ranar Alhamis, ya ce tuni ɗimbin waɗanda su ka yi wa Buhari kamfen “na ta faman yin isrifari ga Ubangiji domin neman gafarar zurɓaɓiyar zaɓen Buhari da su ka sa aka yi.”

Wakilin PREMIUM TIMES wanda ya saurari tattaunawar da BBC ɗin ta yi da Oyinlola, ya ruwaito cewa tsohon gwamnan ya ce, “mun yi kamfen din da aka zaɓi Buhari. Mun yi alƙawurra da dama, amma har yau ko ɗaya ba mu cika ba. Ɗaya daga cikin su shi ne magance tsaro.

“Ganin cewa Buhari tsohon janar ɗin soja ne, sai mu ka yi masa kyakkyawan zaton zai iya magance matsalar tsaro cikin watanni shida idan ya hau mulki. Ashe kallon kitse mu ka yi wa rogo.

“Sai da Obasanjo ya ce mana ya san Buhari, kuma bai da garanti cewa zai iya riƙe Najeriya da kyau. Amma sai mu ka yi tunanin zai ba maraɗa kunya ya daƙile matsalar Boko Haram da ‘yan bindiga.

“Maimakon a samu sauƙi, rabon da Najeriya ta shiga cikin hali firgici irin na yanzu, tun zamanin yaƙin Basasa.”

Oyinlola ya ce babu wani labari yanzu a ƙasar nan kullum idan ka buɗe jarida sai labarin kisa da garkuwa da mutane.

Oyinlola dai ya fice daga APC, ya koma PDP cikin fushi da istigifari, kamar yadda ya jaddada.

Ya ce ya na mamakin cewa “mun yi wa ‘yan kudu alƙawarin sake fasalin mulkin ƙasa, amma yanzu Buhari ya hau mulki, har ya kusa kammalawa, kuma ya yi biris da zancen, kamar bai san da alƙawarin wanda ya ɗauka ba.