SULHU DA YAN BINDIGA YA KARE : Matawalle ya bada umarni a bude wuta ga duk wanda aka gani da makami a Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, a ranar Laraba, ya umarci jami’an tsaro da su harbe duk wani da aka gani da makamin da doka bata amince dashi ba a Zamfara.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar ba zata hedikwatar yan sanda dake babban birnin Jihar, Gusau. Kuma daga bisani ya rubuta a shafinsa na Twitter.

Ziyarar Gwamnan ofishin yan sanda ya biyo bayan kama wasu masu zanga zanga mutum 15 da suka yi zanga zangar nuna fushin rashin tsaro a yankunansu dake karamar hukumar Kaura Namoda.

Matawalle yace jami’an tsaro su aiwatar da dokar da shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bayar cewar a harbe duk wanda aka gani da makami.

Amma yace banda makaman da doka ta amince mutane su rika rikewa.

Gwamnatinmu zata cigaba da taimakawa jami’an tsaro da kayan aiki da sauran abubuwa domin samun nasarar maganin rashin tsaro, inji gwamna Matawalle.

Idan ba a manta ba a baya gwamna Matawalle na daga cikin gwamnonin da ke tada jijiyoyin wuya don ganin an yi sulhu da yan bindiga a yankin Arewa Maso Yamma har da jihar sa.

Matawalle ya rika cewa yin sulhu ne kadai mafita ga hareharen yan bindiga da masu yin garkuwa da mutane.

Sai dai kuma wannan kokari ta sa bata haifar masa da da mai ido ba domin tun ko a lokacin da shi hakan ya ke so, yan bindigan ba su mika wuya ba, sun ci gaba da kai hare-haren su babu kakkautawa, sannan kuma satar mutane ma sai wanda ya karu.

Yanzu dai sulhu ya kare.