Malejin tsadar rayuwa ya ƙara yi wa ƙugun ‘yan Najeriya ɗaurin kalangu, bayan sassaucin watanni takwas

Awon mizanin malejin tsadar rayuwa ta tsawon shekara ɗaya a Najeriya, ya ƙara cillawa sama, bayan sassaucin tsawon watanni da aka samu a jere.

Tsadar rayuwa ta ƙaru da kashi 15.63 a cikin watan Disamba, 2021 idan aka kwatanta ko aka auna ta watan Nuwamba mai kashi 15.40.

Wannan bayani ya fito daga Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa, wadda mallakin Gwamnantin Tarayya ce, a ranar Litinin.

Hukumar, wato NBS ta ce farashin kayan abinci da ayyukan biyan buƙatun dole da na yau da kullum, sun ƙaru da kashi 15.63 cikin Nuwamba, 2021, idan aka auna na watan Disamba 2021, shekara ɗaya baya kenan.

Sannan NBS ta ce idan aka auna canjin farashin kayayyaki tsakanin watan Disamba 2020 da Nuwamba 2021, za a ga cewa farashin ya ƙaru da kashi 1.82 cikin Disamba 2021, alhali adadin ƙarin a cikin Nuwamba 20210, bai wuce kashi 1.08 ba.

Tashin alƙaluman ƙididdigar ya faru ne saboda ƙarin tsadar kayan abinci da aka riƙa samu.

NBS ta ƙara da cewa tsadar kayan abinci ta yi sama zuwa kashi 17.37 bisa 100 a cikin Disamba, 2021.Amma idan aka kwatanta da Disamba 2021, za a ga cewa ƙasa ya yi da kashi 19.56.