ZAZZABIN LASSA: Mutum 48 sun kamu, mutum biyu sun mutu a Najeriya a cikin makon jiya

Alkaluman yaduwar cutar zazzabin lassa da hukumar NCDC ta fitar na makon farko na watan Janairun 2022 ya nuna cewa mutum 48 sun kamu da cutar, mutum biyu sun mutu.

Bisa ga sakamakon gwajin an gano wadannan mutane a kananan hukumomn 20 dake jihohi 10 a faɗin kasar nan.

Jihohi uku da suka hada da Bauchi, Edo da Ondo ne jihohin da suka fi fama da yaduwar cutar a kasar nan.

Sauran jihohin da suke fama da yaduwar cutar sun hada da Taraba, Benue, Kaduna, Filato, Kogi, Cross River da Ebonyi.

Sannan mutu biyu din da suka mutu an gano su ne a jihohin Taraba da Benue.

Daga cikin mutum biyu din da suka mutu daya jami’in kiwon lafiya ne a jihar Benue.

Idan ba a manta ba Hukumar hana yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa an samu ragowa a yaduwa da yawan mutanen da zazzabin lassa ke kashewa a kasar nan a shekarar 2021 fiye da 2020.

Hukumar ta ce a shekarar 2021 mutum 102 ne suka rasu sanady kamuwa da cutar.

Hakan ya nuna cewa Najeriya ta samu ragin kashi 120% a yawan mutanen dake mutuwa a dalilin kamuwa da cutar kasa da yawan da aka samu a 2020.

Zazzabin lassa

Zazzabin Lassa cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cudanyar bera da abincin da muke ci. Wannan cuta dai a sannu a hankali tana ta afkawa mutanen kasar nan.

Ya kan yi wahala a gano cutar a jikin mutum domin ya kan dauki tsawon kwanaki shida zuwa 21 kafin ta bayyana a jikin mutum.

Za a iya kamuwa da wannan cuta idan aka yawaita zama tare da wanda ya kamu da cutar kuma ba a gaggauta neman magani ba.

Alamun kamuwa da cutar sun hada da zazzabi, rashin samun karfi a jiki, zuban jini ta Ido hanci da baki, yawan yin bahaha, amai, Suma da sauran su.

YADDA ZA A GUJEWA KAMUWA DA ZAZZABIN LASSA

1. Tsaftace Muhalli: A rika tsaftace muhalli a ko da yaushe. A kau da datti a kowani lokaci sannan a rika goggoge wuarare.

2. Zubar da Shara: Idan aka tara datti, kada arika barin su kusa da gida. A kai su can wajen da ake zubdawa a nesa ko kuma a rika konawa.

3. Killace Abinci: Yin haka zai taimaka wajen hana bera ko kwari shiga cikin abincin.

4. Dafa Nama: Kafin a dafa nama kamata a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman. A tabbatar naman ya dahu sosai kafin a ci.

Namun Daji: A nesanta kai daga yin mu’amula da namun daji musamman jinsin berayaye da birai.

5. Cin ‘ya’yan itatuwa: Kafin a ci ‘ya’yan itatuwa ko kuma ganye a rika wanke su sosai. Hakan na kau da datti a jikin su.

6. A daina barin dabbobin gida na shiga inda ake aje abinci: Kaji da wasu dabbobin da ake kiwon su a gida kan yi mu’amula da beraye a lokutta da yawa.

7. Toshe kafafen da suka bude: A tabbatar an toshe ramin da bera zai iya shiga cikin dakunan mu.

8. Tsafta: A yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu kafin da bayan an ci abinci sannan idan an kammala amfani da ban daki.

9. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbata sun nemi magani da zarar allurar da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.

10. Kona daji: Kona daji na daga cikin hanyoyin dake koro beraye zuwa cikin gidajen mutane. A rika kiyayewa wajen kona dazukan dake kewaye da mu. Mai makon haka a rika feshin magani.

11. Wanke gawa a cikin Daki: Shima hakan na da illa matuka. Maimakon a rika wanke gawa a cikin gida a rika yin sa a waje ne ko kuma inda ya kamata.