AMAN RAMA SAI AN JA: Yadda EFCC ke gaganiyar zaro naira biliyan 8.5 daga bakin tsohon Shugaban Hukumar NIMASA

A ranar Litinin aka ci gaba da shari’ar da aka gurfanar da tsohon Shugaban Hukumar NIMASA, Patrick Akpobolokemi, wanda ake tuhuma da satar naira biliyan 8.5 a zamanin da ya yi shugabancin hukumsr, daga 2010 zuwa 2015.

Mai gabatar da ƙara ya gabatar da mai shaida na shida a gaban kotu, wanda ya yi wa Mai Shari’a Ayokunle Faaji bayani dalla-dallar yadda ya gano cewa a matsayin sa na jam’in binciken ƙwaƙwaf na EFCC, ya gano cewa waɗanda ake tuhuma ɗin sun yi harƙallar, kuma sa hannun da ke kan takardun da aka riƙa karkatar da kuɗaɗen, duk na ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhumar ne.

Yadda Ake Kama ‘Yan Fashi Da Biro, Ko Da Satar Ta Kai Shekara 50:

Benedict Agweyi, ya ce a matsayin sa na mai amfani da na’urorin bincike a EFCC, “Ofishin Mataimakin Daraktan EFCC da ke Legas ya aika mani da wasu takardu a ranar 25 Ga Afrilu, 2016 domin na yi amfani da na’urori ya tantance wanda ya yi rubutun da kuma wanda ya sa hannu a kan takardun.

“An nemi na tantance takarda mai lamba A1 har zuwa A8. Da kuma mai lamba B1 zuwa B6. Sai kuma C1 zuwa C3.”

Mai bincike Benedict ya kuma shaida wa kotu cewa ba a ba shi sunayen wanda ake zargi ya yi rubutun da kuma sa hannu a kan takardun ba.

Ya ce yanko shafin rubutun da shafin da aka riƙa sa wa hannu kawai aka yi, aka aika masa, shi kuma ya yi binciken da dama aikin sa kenan a hukumar.

“Saboda haka ban san sunan wanda ake tuhuma ba. Ba ni da wata alaƙa da shi, kuma ba ni da wata nifaƙa da shi.”

“Yadda Na Gano Wanda Ya Sa Hannu Aka Kwashe Kuɗaɗen”:

Benedict ya shaida wa kotu cewa hanyoyin bincike uku ne ya yi amfani da su, waɗanda su ka haɗa da:

1. Yin amfani da fensir, na’urar ƙara wa rubutu girma a ido (magnifier), takarda da kuma idanu na da na ke kallon aikin da na ke yi a lokacin.

“Na riƙa bin tartibin farkon rubutu har zuwa ƙarshen sa.

“Kuma na bi diddgin tsarin kowane rubutu domin gano ko akwai bambanci tsakanin rubutun da ke kan takardun ko babu.

“Sannan na bi tare da yin nazarin salon rubutun tare da nazarin yadda aka gina jimla da haɗa kalmomi ko zan ga bambanci ko kamanceceniyar rubutu.”

2. Mataki na biyu da na bi shi ne yin amfani da na’urar da na ƙara girman rubutun har nunki 20 daga girman sa na asali, domin na ƙara ganin su ƙarara, tarwai.

“Sannan kuma na yi nazarin yadda aka riƙa yin rubutun da kuma auna yanayin saurin rubutun da ke kan wannan takarda da wanda ke kan waɗancan takardu domin gano bambanci ko kamanceceniya.”

3. Hanya ta uku da na yi amfani da ita, shi ne yin amfani da bidiyo.”

“Rahoton Da Na Aika Wa EFCC”:

Bayan kammala bincike na, a ranar 31 Ga Yuli 2016, na aika wa ofishin da ya ba ni aikin binciken rahoton cewa:

*Wanda ya sa hannu a kan takardun masu lamba A1 har zuwa A8, da B1 zuwa B6, shi ne dai wanda ya sa hannu kan takardu masu lambar X1 har zuwa X12 da aka gabatar wa Mai Shari’a a matsayin hujja.

*Kuma shi ne dai ya yi sa hannu tare da yin rubutu a kan takardu masu lamba C1 zuwa C13 da aka kawo min su ma na yi bincike a kai.”

Bayan Mai Shari’a ya kammala sauraren mai gabatar da hujja ko shaida Benedict daga EFCC, ya ɗage sauraren ƙarar zuwa washegari, 13 Ga Yuli, 2021.

Waɗanda ake yi wa tuhume-tuhume har 22 tare da tsohon shugaban NIMASA, sun haɗa da Emmanuel Atewe, wani tsohon Manjo Janar, sai Kime Engonzu da wata mai suna Josephine Otuagu.