Maida Dokar Karin Albashi a karkashin jihohi ba za ta yi aiki ba – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa maida dokar karin albashi ta naira 30,000 mafi kankantar albashi daga Tarayya zuwa jihohi, ba za ta biya bukata ba, domin ba za ta iya aiki a karkashin jihohi ba.

Ministan Kwadago Chris Ngige ne ya bayyana haka, a jawabin sa na Ranar Ma’aikata, a Abuja.

Ngige ya ce Dokar Mafi Kankantar Albashi dokar kasa ce ba ta jiha ba. Don haka babu wanda ya isa ya koma gefe shi kadai ya yi mata kwaskwarima, gyaran-fuska ya baddala ta daidai ra’ayin dokokin wata jiha.

“Doka ce da ta hada tarayya, jiha da kananan hukumomi su ka tsara, gwamnati a karkashin Shugaban Kasa aka rattaba mata hannu ta zama doka a ranar 18 Ga Afrilu, 2019. Wannan hannu da Shugaban Kasa ya sa mata, ya tabbatar dokar kenan ta fara aiki tun a ranar.

Ana ci gaba da sa-toka-katsi da wasu gwamnoni cewa ba za su iya biyan mafi kankantar albashi na naira N30,000, sai fa idan ruwan dufanan kudade gwamnatin tarayya za ta rika yi masu duk karshen wata.

Gwamnonin Kano da Zamfara, Abdullahi Ganduje da Bello Matawalle na cikin wadanda su ka ce ba su iya biyan albashi da sabon tsari na naira 30,000 mafi kankantar albashi, sai dai tsohon tsarin albashi na 18,000.

Ngige ys ce sabuwar dokar mafi kankatar albashi ba abu ne da za a iya daukewa daga dokokin tarayya a maida jihohi ba ne. Kuma ba kundin doka ba ne da jihohi za su rika jefa hannu su dauki wadda ta yi masu kyau, wadda ba su so kuma su yi watsi da ita.

“Mun yi kokari mun samar da dokar mafi kankantar albashi daga naira 18,000 zuwa naira 30,000. Don haka babu mai iya canja ta.” Inji Ngige.

Tun da farko Shugaban Kungiyar NLC ta Kasa Ayuba Wabba, ya ce matsawar aka yi gangancin daukar dokar mafi kankantar albashi daga tarayya zuwa jiha, za a fuskanci cirjiya, bore da hargitsi a kasar nan.

Ya ce mafi kankantar albashi doka ce ta kariya da rage radadin talauci ga kananan ma’aikata.

Ya kara da cewa kasar nan sama da mutum miliyan 20 sun afka kuncin rayuwa lokacin kullen korona. Shi ya sa ake kokarin samar wa ma’aikata kandagarkin rage kuncin rayuwa ta hanyar tabbatar da dokar karin mafi kankantar albashi.