Gwamnonin Najeriya sun kassara tsarin shari’a da kotunan kasar nan -Agbakoba

Tsohon Shugaban Kungiyar Lauyoyin ta Kasa, Olisa Agbakoba, ya bayyana cewa gwamnonin Najeriya sun dagula, sun lalata kuma sun gurgunta tsarin shari’a a kasar nan.

Da ya ke magana a ranar Asabar a Lagos, Agbakoba ya ce, “na yi farin cikin ganin Gwamna Kayode Fayemi na kan batun. Saboda zancen gaskiya gwamnoni ba su bin umarnin kotu kwata-kwata.

“Na je kotu na shigar da kara kan ‘yancin cin gashin kan kotuna daga gwamnatin jihohi, kuma na yi nasara a kotu. Amma gwamnonin babu ruwan su da bin umarnin kotu.

“Gwamnonin nan sun kassara tsarin shari’a, sun yi amfani da ikon su sun karya karfin ikon kotu. Saboda ba su dauki ikon su da daraja ba, shi ya sa ba su maida umarnin kotu wani muhimmin batu ko hukunci mai karfin iko ba.” Inji Agbakoba.

Tun a ranar 6 Ga Afrilu ne ma’aikatan kotuna ke yajin aiki a fadin kasar nan, su na neman a bai wa kotuna cin gashin kan kudaden su kai-tsaye.

Tuni harkokin shari’u su ka rincabe, yayin da dimbin daurarrun da su ka kamata kotu ta bayar da belin su, hakan bai yiwu ba, saboda kotunan kasar nan na kulle.

Agbakoba ya yi nuni da matsalar tsarin siyasar da Najeriya ke bin turba, tare da cewa akwai bukatar a sake lale. Har cewa ya yi Najeriya za ta iya rubuwa a cikin ruwan sanyi, idan har an amince ta rabu din.

Agbakoba ya ce shi bai ma gamsu da batun sake fasalin Najeriya, saboda ma’anar da ‘yan kudu ke bai wa sake fasalin Najeriya, ta sha bamban da da ma’anar da ‘yan Arewa ke bayyanawa.