Ɓarkewar Korona a Turkiyya, Birazil da Indiya, ya sa Najeriya ta tsaurara dokar hana shigowa daga ƙasashen

Sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha ya bayyana cewa a dalilin darkakowar annobar Korona da ya tsananta a kasashen Turkiyya, Birazil da Indiya a ƴan kwanakin nan, Najeriya ta sanar da shirin haramta wa matafiya da suka fito daga ƙasashen Brazil shiga ƙasar saboda annobar korona.

Kamar yadda ya fadi, wannan mataki zai fara aiki ne daga ranar Litinin 4 ga Mayu.

Ya ce haramcin ya shafi duk wani jirgi da ya fito daga wadannan ƙasashe uku ne.

Matakin ya zai kuma hada da biyan tarar dala 3,500 ga jirage da kuma fasinjan da suka shigo kasar nan daga wadannan kasashe, sannan jirgin da ya ɗauko fasinjojin da ba ƴan Najeriya ba zai mayar da su, ko sauka ba za su yi a filin jirgi ba.

Haka kuma idan fasinjojin ƴan Najeriya ne, za a killace su da zaran sun iso kasar na tsawon mako daya.

Kasar Indiya ta shiga cikin rudani da mawuyacin hali yadda korona ta tsananta a kasar.

Ya kai ga mutane da kansu suke nema wa kansu mafita domin gwamnati ma ba ta iya yin komai ba tukunna sannan bata saka dokar hana walwala ba.

Mutane da kansu suke kona ‘yan uwansu da suka rasu.

Haka kasar Turkiyya, ita ce yanzu fada cikin tsananin Korona a duka na hiyar Turai. Gwamnatin Kasar ta saka dokar hana walwala.

Ita ma Birazil tana nan tana fama da sake darkakowar Korona din.