MAI RABON GANIN BAƊI: Ƴan sanda sun ceto mutum 39 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su Zamfara

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa ta ceto mutum 39 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a dajin Karanya dake karamar hukumar Kauran Namoda.
Kakakin rundunar Mohammed Shehu ya sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai a garin Gusau.
Shehu ya ce ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wadannan mutane daga kauyukan dake kananan hukumomin Maru da Bungudu.
Ya ce daga cikin mutum 39 din da aka ceto akwai maza 8, mata 15 sannan a cikin su akwai mata masu jego da Yara kanana 16.
Shehu ya ce rundunar ta yi wannan nasara ne a dalilin hada hannun da rundunar ta yi da sojoji domin farautar ‘yan bindiga a Dabar Magaji dake dajin Kadanya wanda ya taso tun daga karamar hukumar Kaura Namoda zuwa Maradun.
“An kai mutanen asibiti domin duba lafiyar su daga nan za a damkasu hannun shugabannin kananan hukumomin su domin a mai da su garuruwan su.
Bayan haka rundunar operation Hadarin Daji ta kama masu aikata miyagun aiyuka mutum 10.
Daga cikin mutum 10 din da rundunar ta kama akwai mutum 3 dake da hannu wajen yin garkuwa da mutum biyu a ƙauyen Fakon Idi dake Talatan Mafara da Satan wayoyin salula biyu a Gusau.
Rundunar na zargin su da kai wa mutane da Fulani hari a kasuwan Dogon Kade.