KORONA: Akwai yiwuwar mutum miliyan 800 suka kamu da Korona a Afirka ba miliyan 8 ba – Binciken WHO

Sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta gudanar ya nuna cewa adadin yawan mutanen da suka kama cutar korona a Afrika zai ninka yawan da aka gano sun kamu da cutar sau 97.

Tun a lokacin da cutar ta bullo a kasar Masar a shekarar 2020 mutum 11,360,305 ne suka kamu sannan cutar ta yi ajalin mutum 250,000 a Afrika.

Bisa ga sakamakon binciken da WHO ta gudanar akwai yiwuwar cewa mutum miliyan 800 sun kamu da cutar daga cikin mutum biliyan 1.3 din dake zama a Afrika ba tare da an sani ba a watan Satumba.

Abin da binciken ya nuna

WHO ta gudanar da wannan bincike daga watan Janairu 2020 zuwa Satumba 2022 inda sakamakon ya nuna cewa an samu karuwa a yaduwar cutar daga kashi 3% a Yuni 2020 zuwa Kashi 65% a Satumbar 2021.

Shugaban kungiyar WHO reshen Afrika Matshidiso Moeti ta ce haka ya nuna cewa a watan Satumbar 2021 mutum miliyan 800 ne suka kamu da korona a maimakon mutum miliyan 8.2 din da aka rawaito,

Binciken ya kimanta cewa akwai yiwuwar cewa anihin yawan mutanen da suka kamu da cutar ya ninka yawan da aka rawaito sun kamu da cutar sau 16.

World meters ya rawaito cewa ranar Asabar mutum miliyan 500 ne suka kamu da cutar sannan cutar ta yi ajalin mutum miliyan 6.2.

Rashin yin gwajin cutar

WHO ta bayyana cewa rashin mai da hankali wajen yi wa mutane gwajin cutar na daga cikin dalilan da ya sa aka ƙasa gano ainihin yawan mutanen da suka kamu da cutar.

Hukumar dakile yaduwar cutar ta Afrika CDC ta bayyana cewa mutum 103,710,049 ne daga cikin mutum biliyan 1.3 dake zama a Afrika aka yi wa gwajin cutar korona.

A Afrika ta Kudu mutum miliyan 24 ne aka yi wa gwajin cutar daga cikin mutum miliyan 60 dake zama a kasar.

Kasar Masar ta yi wa mutum miliyan 3.6 gwajin cutar daga cikin mutum miliyan 150 dake zama a kasar.

A Najeriya mutum miliyan biyar ne aka yi wa gwajin cutar daga cikin mutum miliyan 200 dake zama a kasar.