MA’AIKATA KO MAZAMABATA?: Yadda Ma’aikatun Gwamnati su ka yi wala-wala da naira biliyan 323.5 cikin 2019 – Rahoton Gwamnatin Tarayya

Ofishin Mai Binciken Kuɗaɗe na Tarayya, ya fitar da sanarwar cewa Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, Hukumomi da Cibiyoyin Gwamnantin Tarayya sun kasa bayyana yadda su ka yi da aƙalla naira biliyan 323.5 a cikin 2019.

Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya 27 ne aka kama da laifin wannan gagarimar harƙalla.

Rahoton ya kama ofisoshi da ma’aikatu da laifin kasa yin cikakken bayanin yadda su ka kashe maƙudan biliyoyin kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba.

Sannan kuma ƙiri-ƙiri sun ƙi maida sauran maƙudan biliyoyin nairorin da ba su kashe ba a ƙarshen shekara a asusun tarayya da ke Babban Bankin Najeriya (CBN).

Binciken da aka gano ya tabbatar da cewa ma’aikatun sun riƙa biyan ma’aikatan su biliyoyin kuɗaɗe a matsayin alawus-alawus, ba tare da neman izni ba.

Sannan kuma sun ƙi maida wa CBN biliyoyin kuɗaɗen da ba su kashe a ƙarshen shekara ba, kamar yadda doka ta tanadar, ta ce tilas a riƙa yi.

Kuma ma’aikatu sun riƙa bada kwangiloli ba tare da bin ƙa’ida ba.

Haka kuma an riƙa dumbuzar miliyoyin kuɗaɗe ana biyan ma’aikata ba tare da an shirya bacar biyan kuɗaɗe ba.

An samu ma’aikatu 20 da laifin sun biya alawus-alawus har na naira biliyan 132.5 ba bisa ƙa’ida ba, kuma ba tare da an amince a biya kuɗaɗen ba.

Kamfanin Buga Kuɗaɗe na Najeriya (Nigeria Printing and Minting Company) ya zabge naira biliyan 97 ya biya kuɗaɗen alawus ba tare da neman amincewa ba.

Hukumar Kula da Manyan Kwalejojin Ilmi na Tarayya da ke da hedikwata a Abuja, ta kashe Naira biliyan 2 ba bisa ƙa’ida ba. Ita ce hukumar da ta fi kashe mafi ƙanƙantar kuɗaɗe.

Wasu ma’aikatu 15 kuma sun ƙi damƙa wa Gwamnatin Tarayya harajin da su ka tara cikin 2019, har na naira biliyan 127.1.

A cikin su, Hukumar Kwastan ta Ƙasa ce ta fi ƙin damƙa wa gwamnatin tarayya abin da ta tara, har Naira biliyan 125.

Ofishin Mai Binciken Kuɗaɗe na Tarayya, ya ce ma’aikatun dai sun karya dokar da ke cikin ƙumshiyar bayanai na 415 a cikin Dokar Sa-ido Kan Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya.