Likita ta gargadi ‘yan Najeriya game da hadarin makanta da cutar glaucoma ke haifarwa

Wata mashahuriyar farfesa a fannin ilimin ido, Adeola Onakoya, ta ce jahilci da tsananin talauci na iya kara yiwuwar kamuwa da cutar glaucoma a kasar nan.

Onakoya ta kuma ce tsofaffin maza ƴan ƙabilar lgbo da Yarbawa sun fi zama cikin hadarin kamuwa da cutar glaucoma.

Ta bayyana haka ne a tron Lacca da aka yi a Jami’ar Legas, mai taken “Glaucoma Care in Nigeria: The Journey So Far.”

Glaucoma cuta ce da ke lalata jijiyar gani na ido. Yawanci yana faruwa ne lokacin da ruwa ya taru a gaban idon, kuma wannan karin ruwan yana kara matsa wa cikin ido, sai ya lalata jijiyar gani.

Onakoya ya ba da shawarar cewa duk tsofaffin lgbo da mazan Yarbawa lallai su gaggauta gwajin cutar glaucoma, don sun fi kowa shiga cikin haɗarin kamuwa da matsalar.

A cewarta, mutane miliyan 2.1 ne ke ɗauke da cutar glaucoma a Najeriya, ɗaya daga cikin biyar na masu fama da cutar glaucoma na makanta; Kimanin mutum 420,000 sama da shekaru 40 sun riga sun makance sanadiyyar cutar.

Onakoya ta kara da cewa rashin sani, da kuma kwararru da za su ma duba nutane marasa lafiya da kuma rashin ingantattun magani na daga cikin dalilan da yasa ake samun ƙaruwar yawan marasa lafiyar ido a ƙasar nan.

Sannan kuma da matsalar ciwon hawan jini, shu ma yana sa a kamu da cutar.

Likitoci sun ba sa shawara domin kauce wa wannan cuta, a rika zuwa asibiti ana duba lafiyar idanu akai akai, sannan kuma a e ka motsa jiki akai akai, da kuma cin abinci mai gina jiki.