Kwastam ta kama tireloli 37 cike makil buhunan shinkafa, da tankuna mai 5 a jihar Ogun

Hukumar hana fasa kwauri ta kasa (NCS) reshen jihar Ogun, ta ce ta kama tireloli 37 na shinkafar gwamnati a sassa daban-daban na jihar Ogun a tsakanin watan Janairu zuwa Yuni.
Rundunar ta kuma ce ta kama manyan motocin dakon man fetur guda biyar (PMS) tare da kama wasu mutane bakwai da ake zargi da yin fasa-kwauri a cikin wannan lokaci.
Shugaban yankin, Bamidele Makinde ne ya bayyana hakan a ranar Talata a wajen wani taro kan ayyukan rundunar a cikin watanni shida da suka gabata a hedikwatarta da ke Idiroko, karamar hukumar Ipokia ta jihar Ogun.
A cewarsa, rundunar ta samu Naira miliyan 93.301 daga harajin shigo da kaya tare da gwanjon motocin da suka kama.
Ya ce wasu daga cikin abubuwan da aka kama sun hada da tayoyin da aka yi amfani da su guda 5,048, bale 390 na kayan gwanjo, motoci guda 61, da motocin alfarma guda biyar, da litar man fetur 173,975, buhu 107, da daurin mandula na ganyen Wiwi 1,595, katan 194 na kwalaben ruwan maganin Kodin da dai sauran su.
Jami’in ya ce rundunar ta kuma kama wasu manyan motocin na Bus guda biyar da aka shigo da su cikin kasar ta kan iyakar Ohumbe.