Kotu ta raba auren shekaru 19 saboda miji na zargin matar sa na kwana da wani bokan ta

Mai Shari’a Olayinka Akomolepe na Kotun Gargajiya ta Ado-Ekiti, ya kashe auren wani dattijo mai shekaru 72 da matar sa Folasade mai shekaru 52.

Dattijon mai suna Adeniyi Adeyemi ya shigar da ƙarar neman a raba auren sa da Folasade, bisa zargin ta na surkulle da ‘yan tsatsube-tsatsube.

Sannan kuma ya ce ta na lalata da wani bokan da ta ke zuwa wurin sa.

Adeyemi ya ce matar sa ta canja domin idan ta fita yin tsatsube-tsatsuben ta, sai ta shafe mako biyu ba ta koma gida ba.

Ya ƙara shaida wa kotun cewa a baya ya taɓa zuwa ya gargaɗi bokan, har ya yi masa alƙawarin ya daina kula matar ta sa.

Da ta ke kare kan ta, Folasade ta shaida wa kotu cewa zargin kwartancin da mijin ta ke wa boka ƙarya ne da sharri irin na gigin-tsufa.

“Ƙarya ya ke yi min. Kuma ni wannan bokan yaya na ya haɗa ni da shi, domin ya yi min maganin kumburin da ke damu na a hannu.

“Duk abin da ya same ni, ai shi mijin ne ke tsine min ni da ‘ya’yan mu biyu. Kuma wannan tsinuwar ce ke bibiya ta har hannu na ya kumbure.”

Mai Shari’a ya ce ya raba auren, tunda ita ma matar ta ce gara a rabu. Sannan kuma ya ce ya fahimci ba za a iya sasanta su ba.

Duk da haka, kotu ta umarci matar ta riƙe ‘yar su mai shekaru 15. Amma Adeyemi ya riƙa biyan kuɗin ciyarwa naira 10,000 duk wata.

Shi kuma wani ɗan su mai shekaru 18, kotu ta ba shi zaɓin zama a hannun wanda ya ke so ya zauna a wajen sa, ko mahaifi ko kuma mahaifiyar sa.