KUTUNGUILAR TIWITA: Malami ya musanta yin barazanar gurfanar da masu amfani da Tiwita

Kwanaki kaɗan bayan caccakar Ministan Shari’a Abubakar Malami kan karya dokar hana amfani da Tiwita shi ma da ya yi, ministan ya musanta zargin yin barazanar gurfanar da waɗanda su karya dokar hana amfani da Tiwita.

Malami ya ƙaryata wannan zargi a wata tattaunawa da jaridar VANGUARD ta yi da shi. Sai dai kuma an haƙƙaƙe cewa Malami ya yi barazanar a baya.

Malami ya ƙaryata zargin bayan kafafen yaɗa labarai sun kama shi da laifin karya dokar hana amfani da Tiwita, irin laifin da ya yi barazanar gurfanar da wasu.

“Kowane ɗan Najeriya na da ‘yancin ra’ayin sa ko ma a ina ya ke a duniya.” Inji Malami.

“Matsayin Najeriya shi ne duk wani ko wani kamfani ko ƙungiya da ya yi amfani da Tiwita, ta hanyar karya dokar hana amfani da ita, to za a gurfanar da shi.”

Ya ƙara da cewa jawabin sa da ya fito daga ofishin sa bai bayar da umarni ga Daraktan Shigar da Ƙararraki ya gurfanar da wata kafar soshiyal midiya kotu ba.

“Amma tabbas za mu yi amfani da doka a kan waɗanda su ka taimaka wa Tiwita yi wa Najeriya barazana a matsayin ta na dunƙulalliyar ƙasa.

“Domin a fili abin ya ke akwai masu amfani da Tiwita waɗanda ba su nufin ƙasar nan da alheri. Su na amfani da Tiwita wajen ƙoƙarin haddasa wa Gwamnatin Tarayya rudani a cikin ƙasa.”

PREMIUM TIMES ta buga labarin zargin da Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ya yi, inda ya bayyana cewa kamfanin Tiwita ya yi ladab, ya nemi zaman sulhuntawa da sasantawa da Gwamnatin Najeriya.

Lai Mohammed ya bayyana wa manema labarai na Fadar Shugaban Kasa halin da ake ciki tun bayan dakatar da Tiwita daga Najeriya.

Lai ya yi karin hasken ne bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa tare da Shugaba Buhari a ranar Laraba.

Ministan ya kara jaddada cewa an karya fukafikin ‘yar tsuntsuwar Tiwita a Najeriya, saboda sun bayar da kofa ga wasu marasa kishin kasa su na amfani da kafar da nufin wargaza Najeriya.

Lai ya ce Shugaban Tiwita ne ya rika daukar nauyin dukkan kudaden da masu shirya tarzomar #EndSARS su ka kashe a lokacin zanga-zangar.

“Sannan kuma Tiwita ta bai wa Shugaban IPOB damar watsa sanarwar mambobin IPOB su rika kashe jami’an tsaro, kuma su rika banka wa kadarorin gwamnati wuta.”

Lai ya ce duk da Gwamnatin Najeriya ta yi ta rokon Tiwita cewa ta cire sanarwar Nnamdi Kanu da ya yi shelar a fara kisan ‘yan sanda ana banka wa kadarorin gwamnati wuta, Tiwita ta yi kunnen-uwar-shegu da kiraye-kirayen.

Daga ya lissafa sharuddan da ya ce tilas sai Tiwita ta cika kuma ta amince da su, kafin a amince ta ci gaba da aiki a Najeriya.