JUNE 12 : Yadda Ƴan Arewa suka gwasale Ƴan kudu, sunki fitowa zanga-zangar ƙin mulkin Buhari

Ƴan Arewa sun ki amincewa da kiran da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka yi cewa duk kasa a fito ayi zanga-zangar kin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda gazawar tsaro da sauran wasu abubuwa.
A cikin Jihohi 19 na arewacin Najeriya jihar Filato da babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja ne kadai suka yi zanga-zangar a ranar 12 ga Yuni.
A madadin zanga-zangar, wasu gwamnatoci a Arewa sun yi bikin murnar ranar dimokaradiya da taron siyasa, su kuma sauran jama’an gari sun ci gaba da sauran harkokin su na yau da kullum kamar yadda suka saba.
PREMIUM TIMES HAUSA ta ruwaito yadda Ƴan zanga-zangar masu goyon bayan mulkin Buhari dana kungiyoyi masu zaman kansu suka amshi na goro a wajen iyayen gidansu kafin yin zanga-zangar a Abuja.
A Kano, PREMIUM TIMES HAUSA ta lura yadda mutane suka gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da amsa kiran yin zanga-zanga ba.
Shi kuma gwamna Abdullahi Ganduje, taron siyasa yayi a filin kwallo na Kano Pillars a inda ya amshi jagajigan ƴan siyasa irinsu Salihu Sagir Takai na jam’iyyar PRP da Abdulsalam Zaura na Jam’iyyar GNP da wasu ƴan kwankwasiyya zuwa APC
Taron ya samu hallartar manya manyan Ƴan siyasa na APC da magoya bayansu. Haka shima shugaban majalisar dokokin Jihar ta Kano Hamisu Chidari ya halarci taron.
A Kaduna, ba’ayi zanga zangar ba kuma an samu karancin zirga-zirgan jama’a saboda ruwan sama da aka kamar da bakin kwarya ba yinin gaba daya.
A jihohin Sokoto, Zamfara, Kebbi , JigawaPREMIUM TIMES HAUSA ta lura yadda mutane suka yi harkokinsu ba tare da yin zanga zangar ba a ranar ta Asabar.
Mataimakin sufeton ƴan sanda mai kula da jihohin Zamfara, Sokoto, da Kebbi, Ali Janga, ya sanar da cewa rundunar Ƴan sanda ta shirya tsaf wajen tabbatar da ba a samu tashin hankali ba a jihohin.
Sannan yayi kira ga malaman addini, sarakuna da iyaye su ci gaba da sa ma ƴaƴan su ido a koda yaushe gudun kada su fada tarkon ƴan sanda.
A Jigawa, Gwamna Muhammad Badaru, yayi amfani da ranar ta June 12 wajen bayyana nasarorin da gwamnatin ta samu da ya jaɗa da samarwa matasaya ayyukan yi a musamman fannin noma.