KURURUWAR MANOMA GA BUHARI: Matsalar tsaro na yi wa aikin noma barazana fa

Wasu manyan manoma da masu harkokin noma da safarar hada-hadar abinci sun yi roko ga Gwamnatin Tarayya ta maida himma da kara zage damtse wajen kokarin dakile ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma Boko Haram, domin su na kawo gagarimar matsala a harkokin noma da samar da wadataccen abinci a kasar nan.

Sun bayyana cewa yawan hare-hare da kisan da ake wa manoma da garkuwa da su na haddasa su kaurace wa gonaki, wasu ma su na yin hijira zuwa wasu garuruwa daban domin tsira da rayukan su.

Shugaban Hukumar NALDA, Paul Ikonne, ya ce akwai matukar shawo kan matsalolin tsaro da gaggawa a kasar nan, idan ba haka ba kuwa, to ‘yan bindiga su su haddasa gagarimar matsalar karancin abinci a kasar nan.

Ikonne ya na ganin cewa a zauna a samu maslaha da fahimtar juna tsakanin makiyaya da manoma zai iya samar da zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.

“Ni dai na tabbata cewa manoma na bukatar shanun su su ci abinci da ciyawa su yi bul-bul, yadda idan za su sayar su samu kudi da yawa. Wato su na bukatar zaman salama da zumunci tsakanin su da al’umma, ba tare da tashin hankali ba.

“Saboda haka NALDA za ta tuntubi bangarorin biyu da mutanen yankunan karkara domin samar da yanayin da manoma da makiyaya za su zauna lafiya da juna.” Inji shi.

Shi ma Shugaban Manoma Masara na Najeriya, Bello Abubakar, ya ce duk da a yanzu su na noma masarar da za ta wadaci kasar nan, akwai bukatar kara samar da tsaro don kada nan gaba kadan a samu koma baya.

Ya ce idan ana bukatar manoma su kara himma, to tabbas sai fa an kawar da matsalar ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda.

“A yanzu manoma da dama ba su iya zuwa gona, saboda su na tsoron kada a sace su, ko a yi masu fashi a kwace masu dukiya ko kuma a kashe su dungurugum baki daya.” Inji Abubakar.

Sai ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da haramta shigo da masara cikin kasar nan, domin hana shigo da ita daga waje ya na karfafa wa manoman ta na nan cikin gida guiwar mikewa tsaye su bunkasa noman masara a kasar nan baki daya.

Ita ma Shugabar Hadaddiyar Kungiyar Mata Manoma ta Kasa, Salamatu Garba, ta ce duk da gagarimar matsalar tsaron da ake fuskanta, manoma da dama na saida rai su na gaganiyar noma abincin da zai ciyar da kasar nan.

Ita ma ta yi kIran a kara karfafa tsaro domin karin samun wadatar abinci.

Kamar Salamatu Garba, shi ma Shugaban Kungiyar Masu Chasar Shinkafa na Kasa, Peter Dama, kira ya yi a kara matsa kaimi wajen inganta tsaro domin a kara samun wadatar abinci a kasar nan.