Eid-El-Fitr: Mataimakin Gwamnan Kebbi ya yi ƙira da a zauna lafiya

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

A sakonsa na taya murnar ƙaramar Sallah (Eid-El-Fitr) wanda ya samu sa hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin sadarwa na Zamani Atom Turba Ishaku, Mai girma, Dr Sama’ila Yombe Dabai mni (Tambarin Zuru), Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi ya ƙirayi al’ummalar musulmi na duk duniya da su zauna lafiya tare da ci gaba da nuna kyawawan aiyuka da halaye irin na wanda suka kasance suna yi ciki wata Ramadan.

Da yake ganawa da manema labarai bayan Sallar Eidi a ranar Alhamis, Dakta Samaila Yombe Dabai ya yi amfani da wannan dama wajen yabawa da ƙoƙarin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Bagudu na jihar Kebbi.
Mataimakin Gwamnan ya ƙara da aika saƙon yabo da jinjina ga Sarakunan jihar kan irin goyon bayan da suke bai wa manufofi da shirye-shiryen Gwamnatin jihar a koyaushe.
Game da halin rashin tsaro a jihar musamman a Kudancin jihar, Sama’ila Yombe Dabai ya jaddada cewa Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ba zai yi ƙasa a gwiwa ba kan kokarin da Gwamnatin jiha ke yi na dorewar zaman lafiya, yana mai amfani da wannan dama wajen yin ƙira ga miyagun mutane da ke kai hare-hare a kan al’umma da su dakatar ko kuma su fuskanci fushin doka.
Mataimakin Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jiƙan dukkan waɗanda suka mutu, ya sa can ya fi musu nan.

Raarraba

Facebook

Twitter

Labarin bayaMatar gwamna ta rabawa dubban mata kuɗi da kayan Sallah a Zamfara