KADUNA: Kungiyar kwadago ta umarci tashoshin jirgin Sama da Kasa, ma’aikatar raba wutar lantarki da ma’aikatan jibar kaf su fara yajin aiki daga yau

Mutanen jihar Kaduna za su shiga cikin matsanancin hali da ranar Asabar a dalilin umarni da kunguiyar kwadago ta bada na ma’aikata su fara yajin iki na gama gari a jihar Kaduna.

Hakan ya biyo bayan gargadi da kungiyar ta baiwa gwamnatin jihar ta janye daga shirin korar ma’aikata da ta yi niyyar yi tunda wuri ko kuma gaba daya tun daga Abuja a yo mata gangami har sai ta dakatar da wannan nufi na ta.

Kamar yadda sanarwar ya kunsa, daga ranar Asabar din yau, kungiyar ta umarci, kada jirgin sama ya sake tashi daga filin sama na Kaduna, jirgin kasa ya dakatar da ayyukan sa kaf a jihar.

Haka kuma Hukumar rarraba wutar lantarki ta kasa, ita ma ta tabbata ta kashe wutan lantarki da ake sha a duk fadin jihar har sai illa ma sha’Allah.

” Wannan gargadi ne mai mahimmanci. Da mai’aikata da hukumomi duk gaba daya kaf ba za su yi aiki a Kaduna ba daga yau Asabar. Babu wuta, babu sufurin jirgin sama da na kasa, komai zai tsaya cak da yau Asabar har sai El-Rufai ya dakatar da shirin korar dubban ma’aikatan jihar.

‘Yan Kaduna dai sun ga tasko, domin a halin da ake ciki gwamnati ta ce taji ta gani, shege ka fasa.