A KWANA CIKIN SHIRI: Gagarimar annoba da tafi Korona bala’i na nan darkakowa – gargaɗin WHO

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi kira ga kasashen duniya da kowa ya zauna da cikin shirin bullowar wata cuta da ta fi Korona bala’i.

Shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya yi wannan gargadi a zaman jami’an lafiya na duniya karo na 76 da aka yi a Geneva kasar Switzerland.

“ Akwai alamun bullowar wata cuta da alamun ta ya fi illa fiye da kowacce cuta sannan tana da saurin kisa.

“ Ya zama dole gwamnatocin duniya su mike tsaye domin tsara hanyoyin samun kariya musamman a wannan lokaci da muke ciki.

Wannan gargadin ya fito ne bayan mako daya da shugaban WHO ya sanar cewa Korona tashi daga annoba.

Ghebreyesus ya ce wannan zaman da WHO ta yi zama ce da aka Yi domin Yi wa kasashen duniyan gargadin inganta fannin kiwon lafiyar su domin samar wa mutanen su kariya a duk lokacin da wata cuta ya bullo.