KOWAR HAƊIYI TAƁARYA: Shugaban APC ya gana da Sanatocin APC domin magance fitar-farin-ɗango da ake yi daga jam’iyyar

Ganin yadda hasalallu daga sama har ƙasa ke ci gaba da yin fitar-farin-ɗango daga APC zuwa wasu jam’iyyu, Shugaban jam’iyya mai mulki Abdullahi Adamu ya garzaya Majalisar Dattawa domin yin ganawar sirri da Sanatocin APC, a ƙoƙarin shawo kan ci gaba da ficewar da ake yi a kullum.
Adamu ya isa Majalisa kusan ƙarfe 2 na yammacin Laraba, inda ya yi ganawar sirri da Sanatocin.
Bayan ya fito, ya shaida wa manema labarai cewa canjin sheƙar fitar-farin-ɗango da ake yi daga APC abin damuwa ne.
Ya ƙara da cewa dalili kenan ya je Majalisar Dattawa ya gana da Dattawan APC, domin shawo kan lamarin.
“Shugabannin jam’iyya na ƙoƙarin samo hanyar hana ci gaban ficewar. Babu jam’iyyar da ba a fita. Amma an fi zuzuta ficewar da ake yi daga APC. Amma duk da haka mun damu sosai, saboda ruwan da ya doke ka, shi ne ruwa.”
An fara rubdugun ficewa daga APC tun bayan kammala zaɓen fidda-gwani, inda aka riƙa ƙorafin yin rashin adalci da maguɗi tun daga sama har ƙasa.
Shi kan sa Adamu ana zargin sa haddasa rikicin da ke faruwa yanzu, wanda APC ta miƙa wa INEC sunan Sanata Ahmad Lawan wanda bai tsaya takara ba, maimakon sunan Basheer Machina, wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na mazaɓar Lawan.
Kusan sati ɗaya kenan a kullum sai Shugaban Majalisar Dattawa ya bayyana ficewar aƙalla Sanata ɗaya daga APC.
Cikin hasalallun Sanatocin da su ka fice daga APC sun haɗa da Shugaban Masu Rinjaye, Yahaya Abdullahi, Adamu Aleiro, Francis Alimekhena, Babba Kaita mai wakiltar Mazaɓar Shugaba Buhari, Halliru Jika da kuma Lawan Gumau.
Wannan jarida ta kuma buga yadda zaɓen fidda-gwani ya janyo ficewar jiga-jigan APC a Katsina, Sokoto da Bauchi.
A Jihar Bauchi manyan APC su shida, waɗanda su ka haɗa ‘yan Majalisa da tsohon mataimakin gwamna, sun fice daga jam’iyyar APC a jihar Bauchi. Kuma ba su kaɗai su ka fice ba, har da ɗimbin magoya bayan su duk su ka yi gaba, su ka bar APC cikin ruɗani a Bauchi.
Ficewar manyan APC daga jam’iyyar a Bauchi ya kawo cikas ƙwarai ga ƙoƙarin da ta ke yi na karɓe mulki daga hannun PDP, wadda Gwamna Bala Mohammed ya sake tsaya mata takara, domin ya kammala zangon sa na biyu kuma na ƙarshe.
Guguwar canjin sheƙa ko guguwar ficewa daga APC ba a Bauchi kawai ta tsaya ba. Hasalallu daga jihohi daban-daban na ci gaba da yin tururuwar ficewa daga APC su na shiga wasu ‘jam’iyyun daban.
Babban dalilin ficewar mafiya yawan su shi ne zargin rashin adalcin da su ke cewa an tafka masu yayin zaɓen fidda-gwani.
Hasalallun Da Suka Fita APC A Jihar Bauchi:
Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu, Lawal Gumau ya fita daga APC ya koma NNPP, bayan ya kasa lashe zaɓen fidda-gwani.
Shi ma Sanata Halliru Dauda ya canja sheƙa, bayan ya kasa cin zaɓen fidda-gwanin takarar gwamna.
Sai kuma Ɗan Majalisar Tarayya na Bauchi, shi ma ya fice bayan ya kasa cin zaɓen fidda gwani.
Tsohon Mataimakin Gwamna, Abdu Sule ya fice saboda abin da ya kira rashin dattako da rashin sanin ya-kamata da ake nunawa a APC.
Akwai Farouq Mustapha, Ibrahim Mohammed da sauran su.
Katsina: Yadda NNPP Ta Kwashi Lodin Mutanen Buhari:
Akwai Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Malumfashi/Ƙafur, Babangida Talau, Armaya’u Kado mai wakiltar Dutsin-Ma/Kurfi, Aminu Ashiru mai wakiltar Mani/Bindawa.
Hadimin Aminu Abdulƙadir mai suna Bature Ibrahim ya ce “Oga na zai sake shiga takara ya kare kujerar sa a ƙarƙashin NNPP.
Shi kuma Talau takarar Sanata ya fito a ƙarƙashin NNPP a shiyyar Sanatan Katsina ta Kudu.
Akwai tsoffin ‘yan takarar gwamna biyu, Umar Abdullahi (Tata) da Garba Ɗanƙani, duk sun fice daga APC.
Umar ya koma PDP, shi kuma Ɗanƙani takarar gwamna zai yi a ƙarƙashin AA.