‘Kowa Ya koma Gona’, amsar Buhari da aka ce masa bai taɓuka komai a bunƙasa tattalin arziki ba

Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙi yarda da iƙirarin cewa gwamnatin sa ba ta taɓuka komai a fannin Inganta tattalin arzikin ƙasa ba.

Ya bayar da amsar cewa mafitar ƙasar nan daga ƙalubalen tattalin arziki shi ne a koma gona a rungumi noma.

Haka ya faɗa a tattaunawar da Gidan Talabijin na Channels ya yi da shi, wadda aka nuna a ranar Laraba da dare.

A cikin tattaunawar sa da Seun Okinbaloye da Maupe Ogun-Yusuf, Buhari bai yarda da wasu alƙaluman ƙididdigar da matambayan biyu su ka bijiro masa da su ba, waɗanda su ka nuna masa cewa tattalin arzikin Najeriya tafiyar-kura ya ke yi tun bayan da Buhari ya hau mulki cikin 2015.

Cikin tattaunawar, an baje wa Buhari tantagaryar ƙididdiga da jadawalin tsadar rayuwa da taɓarɓarewar tattalin arziki tsakanin 2015 zuwa 2021.

Tambaya: Lokacin da ka hau mulki cikin 2015, bashin da ake bin Najeriya bai fi naira tiriliyan 12 ba. Amma a yanzu daga hawan ka har ya kai wajen naira tiriliyan 32.”

Buhari ya ƙi yarda da alkaluman da ‘yan jaridar suka bijiro masa da su, amma kuma bai kawo nasa alƙaluman an gware ba. Sai dai ya ce maganin matsalar ita ce ‘yan Najeriya su koma gona.

Buhari ya sake yin kira ga ‘yan Najeriya “su riƙa cin abincin da su ke nomawa da kuma noma abin da za su riƙa ci.”

Ya buga misali da cewa a yanzu a Najeriya ake noma shinkafar da ake ci, har ma ake fitar da ita waje.

Sai dai kuma kayan abinci yawanci duk farashin su ya nunka bayan hawan Buhari mulki. Shinkafar ma ta gida har ta na neman ta gagari talaka.