‘Rudu da hauragiyar ‘yan siyasa ne kawai wai zan koma APC, amma kuma fa bari muga yadda gaba zata kasance’ – Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa maganar wai zai koma APC duk rudu ne da hauragiyar ‘yan siyasa amma shi bai koma ko-ina ba, yana nan a PDP kuma ko shawarar canja sheka bai yi ba.

Kwankwaso ya kara da cewa ziyarar ta’aziyya da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yayi ziyara ce ta ta’aziyya ba ta wai sulhu da ake ta rade-radin wai sun yi ba.

“Ita ma wannan magana ba gaskiya bace sai dai kuma mutumin da ya ziyarceka domin yi maka ta’aziyya ai dole ka karbe shi hannu bibbiyu.

Kwankwaso yayi wannan bayani ne a hira da yayi da tashar DW Hausa ranar Alhamis.

Idan ba a manta ba tun bayan zaman sa gwamnan jihar Kano, Ganduje da Kwankwaso suka rika kai ruwa rana a tsakanin sa da Rabiu Kwankwaso.

Dukkan su su biyun sun rika fitowa kafafen yada labarai suna sukan juna da ya kai ga sai zaman tsama a tsakanin su yayi tsananin gaske.

” Mun shiya ko bamu shirya ba Ganduje ya zo min ta’aziyyar rasuwar dan uwa na, wannan shine.