Dalilin da ya sa ba zan tsoma baki a saki Nnamdi Kanu ba -Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai tsoma baki ya ce a saki Nnamdi Kanu ba, saboda yin hakan katsalandan ne a cikin fannin shari’a.

Haka Buhari ya furta a wata tattaunawa da aka yi da shi a Gidan Talabijin na Channels, wadda aka nuna a ranar Laraba da dare.

“Akwai hukuma ɗaya wadda ba zan taɓa yi mata katsalandan ba. Ita ce ɓangaren shari’a.” Inji Buhari.

“Mun ba shi damar da zai kare kan sa a Najeriya, maimakon ya riƙa surfa mana zagi daga Turai.”

Da ya ke magana, Buhari ya ce ba za a saki Nnamdi Kanu ba, sai dai ya kare kan sa a kotu kawai.

“Masu cewa a saki Nnamdi Kanu, to ba za a sake shi ba, saboda ba zai yiwu ka riƙa aika saƙonnin da ba gaskiya ba ne a kan tattalin arzikin ƙasa da tsaron ƙasa, sannan kuma ka ce wai ba za ka girbi abin da ka shuka ba.”

Shari’ar Kanu Da Ziyarar Dattawan Igbo Fadar Shugaban Ƙasa:

Watanni biyu da suka gabata ne wannan jarida ta buga labarin yadda dattawan ƙabilar Igbo su ka faɗi ba nauyi, su ka tashi ba nauyi a gaban Buhari, yayin ziyarar neman a saki Kanu da suka kai Fadar Shugaban Ƙasa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa wasu dattawan ƙabilar Igbo cewa ba zai shiga hurumin ɓangaren shari’a ba, domin ya saki Nnamdi Kanu, wanda a yanzu batun tuhumar da ake masa na kotu.

Buhari ya yi wannan furucin ne yayin wa wasu gungun manyan dattawan ƙabilar Igbo su ka kai masa ziyarar roƙon ya saki Nnamdi Kanu da ke tsare.

Nnamdi Kanu, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar IPOB masu rajin ɓallewa daga Najeriya ko da tsiya, ya shiga hannun hukuma ne yayin da aka kamo shi daga waje, bayan ya tsallake ƙasar nan daga belin sa da aka bayar.

Shugaban tawagar mai suna Mbazulike Amaechi, ya shaida wa Buhari cewa sun zo ne domin su roƙe shi alfarmar ya saki Nnamdi Kanu domin a samu zaman lafiya a yankin Kudu maso Gabas.

Mbazulike, wanda dattijo ne mai shekaru 93 a duniya, ya shaida wa Buhari cewa a cikin ministocin da aka yi a Jamhuriya ta ɗaya, shi kaɗai ne ya rage a duniya.

“Ina roƙon Shugaban Ƙasa ya yi alfarmar cewa idan ya saki Kanu, ni da kai na zan sa masa takunkumin hana shi yin irin kalaman ɓatuncin da ya ke yi.

“Na kasance dattijon da ake girmamawa a Yankin Kudu maso Gabas sosai. Ina roƙon a ba ni shi domin dama ce ta samar da zaman lafiya a yankin mu.

“Ya mai girma Shugaban Ƙasa, yankin mu ya shiga cikin gagarimar matsala saboda tashe-tashen hankulan da ake yi dalilin IPOB.

“Harkokin tattalin arziki sai ja baya su ke yi. Ga kuma harkar ilmi ta shiga garari. Matsalar tsaro kuma sai ƙara ƙamari ta ke yi.

“Na yi amanna da cewa a bi matakin diflomasiyyar siyasar cikin gida a wanzar da zaman lafiya a yankin shi ne mafi alheri, ba amfani da ƙarfin soja ba.

“Ba zan yi fatan na mutu na bar yankin mu cikin tashin hankalin da ya ke ciki ba a yanzu.

“Shugaban Ƙasa wannan dama ce gare ka cewa idan ka saki Kanu, ka zama shugaban da ya samu yankin mu ciki rikici, amma ya wanzar da zaman lafiya a yankin.”