Kotu ta wanke tsohuwar Ministar Buhari daga zargi

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta wanke tsohuwar Ministar Kuɗi, Misis Kemi Adosun daga takaddama kan ta yi wa ƙasa hidima (NYSC) ko akasin hakan.

A yayin da yake yanke hukunci a zama na yau Laraba kan ƙarar da aka shigar gaban kotun, mai shari’a Taiwo Taiwo, ya bayyana cewa Adeosun ba ta cancanci ta yi wa ƙasa hidima ba a lokacin da ta kammala karatun ta na shekaru 22, saboda a lokacin ita mazauniya ƙasar Ingila ce.

Alkalin ya ci gaba da cewa har zuwa lokacin da ta dawo gida Najeriya, kuma ta zama ‘yar Najeriya, shekarunta sun zarce 30, dan haka ba ta cancanci yin hidimar NYSC ba.

Mai Shari’a Taiwo ya ce mai shigar da karar ko wani ba ya bukatar takardar shedar sallama ta NYSC don cancantar tsayawa takarar kujerar siyasa ko samun muƙamin naɗi a siyasa.