Majalisar Dattawa ta amince Buhari ya sake ciyo bashin N2.3trn

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Gwamnatin Tarayya na neman rancen dala biliyan 6.1 wanda ya yi daidai da naira tiriliyan (N2.343 trillion).

Majalisar dattijan ta tabbatar da amincewar ne a zamnata na yau Laraba bayan ta yi la’akari da rahoto da kwamitinta dake kula da ciyo bashi ta gabatar a gabanta wadda ta sanya ta a kwanakin baya ta yi aiki a kan neman ciyo baahin.

Da yake gabatar da rahoton a zauren majalisar yayin zaman yau, Shugaban kwamitin, Sanata Clifford Ordia ya ce bukatar ba sabuwa ba ce domin an zayyana a cikin kasafin kuɗin 2021 inda ya ce za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen aiwatar da gibin kasafin 2021.

Shugaba Muhammadu Buhari a farkon watan Mayu ya roki Majalisar Dokoki ta kasa ta amince da bukatar rancen, yana mai cewa za a karba daga bangarori da dama ciki har da kasuwar hadahadar ƙasashen duniya