ANA WATA GA WATA: Jam’iyyar APM ta garzaya kotu, ta nemi a ƙwace nasarar Tinubu a bai wa Atiku da ya zo na biyu

Jam’iyyar ‘All Peoples Movement’ (APM), ta ce takarar Bola Tinubu na jam’iyyar APC da ya yi nasara, haramtacciya ce, domin ba a bi ƙa’iba wajen zaɓen ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Tinubu, wato Kashim Shettima.
APM ta bi sahun su PDP da LP, ta maka APC da INEC ƙara ranar 20 Ga Maris, ta na so Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓe a Abuja ta bayyana Atiku Abubakar a matsayin wanda ya zo na biyu, cewa shi ne ya yi nasara, kuma shi ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, ba Tinubu ba.
A ranar 1 Ga Maris ne aka bayyana cewa Tinubu ya yi nasara.
A cikin kwafen takardun ƙarar da APM ta shigar, ya ce Tinubu bai shiga takara bisa ƙa’ida ba, saboda Kashim Shettima bai cancanci tsayawa takara ba.
Idan ba a manta ba, lokacin da Tinubu ya fito takara, ya miƙa sunan Ibrahim Masari a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Ibrahim Masari ɗan Katsina ne, jihar Shugaba Muhammadu Buhari. An ajiye shi ne matsayin ɗan takarar wucin gadi, kafin zaɓen mataimaki, wanda aka ɗauki Shettima daga baya.
Masu sharhin siyasa maganin Tinubu ya ɗauki Ibrahim Masari ne don cika umarnin INEC cewa ranar 27 Ga Yuni ce za ta rufe karɓar sunayen ‘yantakara, wato ranar 17 Ga Yuni, 2022.
A ranar 10 ga Janairu Ibrahim Masari ya janye, Aka maida sunan Shettima.
A Daura Tinubu ya bayyana sunan Shettima matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, yayin da ya kai wa Buhari ziyasa.
A kan haka ne APM ta ce Shettima ya fito takara a wurare biyu, wato takarar sanata da ta mataimakin shugaban ƙasa a lokaci guda.
“Har zuwa ranar 25 ga Yuli, 2022, akwai sunan Tinubu a cikin masu takarar sanatoci.”
APM ta ce ta samu kwafen takarda daga INEC a ranar 14 Ga Yuli cewa a ranar an canja sunan Ibrahim, aka maye gurbin sa da na Ibrahim.
APM ta ce Sashe na 131(C) da 142 ya nuna Ibrahim Masari ne ɗan takarar mataimakin Tinubu, tunda ya janye kuwa, takarar Tinubu ta faɗi kenan.
APM ta ce Sashe na 131(C) da 142 na doka ya nuna Tinubu ba ɗan takara ba ne, domin ba ya halatta ya tsaya takara ba da mataimaki ba.
Waɗannan da wasu dalilai ne ya sa APM ta nemi kotu ta kwace nasara daga hannun Tinubu ta bai wa Atiku Abubakar na PDP da ya zo na biyu.