KORONA: Yadda dubban fasinjojin jiragen da ya kamata a killace daga sauka ke sulalewa cikin jama’a – Gwamna Sanwo-Olu

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana cewa kashi 18 na fasinjojin da su ka shigo Najeriya ta jirage daga ƙasashen waje, duk sun sulale cikin jama’a, ba tare da an killace su kamar yadda dokar daƙile korona ta gindaya ba.

Dokar dai ta ce duk wanda ya shigo Najeriya daga ƙasashen indiya, Afrika ta Kudu, Brazil da Turkiyya, to tilas sai an killace shi kafin a bar shi ya shiga cikin jama’a.

To sai dai a Najeriya wannan ƙa’ida ba ta yi tasiri ba, domin Gwamnan Legas ya bayyana cewa “tsakanin watan Mayu zuwa 7 Ga Yuli, 2021 aƙalla fasinjojin jiragen sama har mutum 50,322 sun shigo Najeriya ta filin Jirgin Legas. Amma kashi 18 daga cikin su duk sun sulale ba tare da an killace su ba.

Sanwo-Olu ya ƙara da cewa wasu da dama sun bayar da adireshin lambar gida na bogi. Wasu kuma hatta lambobin wayar da su ka bayar domin jami’an lafiya na EKOTELEMEN su tuntuɓe su, duk na bogi ne.

Gwamnan ya jaddada cewa daga yanzu duk ɗan ƙasar wajen da aka kama ya bijire wa dokar killace matafiya, to za a ƙwace bizar sa sannan kuma a ci shi tara.

Idan ɗan Najeriya ne kuwa, za a hukunta shi dai-dai yadda dokar kullen korona ta 2020 ta tanadar.

A ƙarshe Sanwo-Olu ya ce korona samfurin ‘Delta’ ta kutsa cikin Lagos.

Ya yi gargaɗin jama’a kowa ya kiyaye, ya ci gaba da ɗauka takunkumi, a riƙa wanke hannaye a kuma daina cakuɗeɗeniya a cikin cinkoson jama’a.