An damƙe wanda ya ɗauki nauyin kashe Shugaban Haiti don ya maye gurbin sa

Shugaban ‘Yan Sandan Ƙasar Haiti ya bayyana wa manema labarai cewa an kama wanda ya ɗauki nauyin kashe Shugaba Jevonel Moise.

Wanda aka damƙe ɗin ɗan ƙasar Haiti ne da ke zaune a Jihar Florida a Amurka.

Jihar Florida ta haɗa iyaka da Haiti, kuma nisan kilomita 1,000 ne tsakanin jihar da babban birnin ƙasar Haiti.

Shugaban ‘Yan Sanda ya shaida wa ‘yan jarida cewa an samu hujjar cewa likitan daga Florida ya ɗauki nauyin kisan, domin an samu tabbacin cewa ɗaya daga cikin makasan da aka kama ya yi waya da shi, jim kaɗan bayan bindige Moise.

“Sannan kuma an samu wasu hujjoji a gidan sa.”

An dai kama shi a Haiti, domin bayan an yi kisan, ya hanzarta ɗauko shatar jirgi ya diro Haiti domin ya karɓi mulki.

Wanda ake zargin ya na da shekaru 63 a duniya. Ya yi amfani da sojojin hayar Venezuala su ka yi masa hayar sojojin haya daga Columbiya, su ka bindige Shugaban Haiti a cikin gidan sa.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin kisan makonni biyu da su ka gaba.

Ta buga cewa mahara sun kutsa gidan Shugaban Haiti, sun bindige shi.

Wasu mahara da ba a gane su ba, sun kutsa cikin gidan Shugaban Ƙasar Haiti sun bindige shi.

Lamarin ya faru wajen ƙarfe ɗaya na daren wayewar garin Laraba, kamar yadda Shugaban Riko kuma Firayi Minista Claude Joseph ya bayyana a cikin wata sanarwa.

Ya ce maharan sun kashe Shugaba Jovenel Moise kuma matar sa Martine Moise ta samu raunuka. Yanzu haka ta na kwance asibiti.

An ce wasu daga cikin maharan an ji su na yaren Sifananci. Amma har yanzu ba a tantance su wa su ka kai mummunan harin ba.

Ƙasar Haiti mai jama’a miliyan 11 da ke yankin ƙasashen Carrebean, ta shiga cikin ruɗani tun bayan zaɓen da aka nemi yi amma abin ya kakare.

A yanzu dai Firayi Minista Joseph ya ce shi ke wa ƙasar riƙon ƙwarya, kafin a nan mafita nan gaba.

Ana zaton baƙin haure ne su ka haura gidan shugaban su ka harbe shi.