Cin kofi da saura wa Ingila duk da shafe shekaru 55 tsit

A wasan karshe da aka buga tsakanin Kasar Ingila da Italiya, Italiya ce ta yi nasara a bugun daga kai sai gola da ya kai ga kasashen biyu.

Rabon da Ingila ta ci wani babban gasa a duniya shekaru 55 kenan dalilin da ya sa suka daura damaran ko ana ha maza ha mata za su kawo karshen wannan zaman rashin Kofi da kasar ke yi.

Tun bayan saka kwallon daya da Ingila ta yi cikin minti biyu da fara wasa yan italiya suka rika surfar Ingila kamar bayin su.

An taka leda kamar ba a yi ba, daga karshe dai haka aka yi ta haure-haure har aka tafi hutun rabin lokaci.

Dawowar su ke da wuya, sai Italiya ta rama wannan kwallo daya.

Tun da Italiya ta samu ta maida wasan daya da daya, sai ta datse bayan ta, yan wasan gaba kuma suka tsima, sai harikawai suka kai wa kasar Ingila a filin su, ta Wembley.

Haka da aka yi har minti 90 ya cika.

Alkalin wasa ya kara minti 30 kamar yadda aka saba yi idan ya sa ya kara a kunnen doki.

Nan ma haka aka yi da taka leda kwallo bai shiga ragar kowa ba.

A bugun daga kai sai mai tsaron raga, kuwa nan ne yaran Ingila suka zubar da kwallaye 3, iat kuma Italy ta zubda 2.

An yi bakin ciki matuka a Ingila domin sun sa ran lashe gasar ganin a kasar su ake buga wasan karshe.