KORONA: Tabbas Nau’in Omicron na kisa da jikkita mutane idan aka kamu – Inji WHO

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa nau’in Omicron na jikkita mutane idan suka kamu kuma tana gaggawar aika wa da mutum lahira idan ba a shawo kanta da wuri ba.

Shugaban hukumar Tedros Ghebreyesus ya sanar da haka ranar Alhamis a taron da ya yi da manema labarai kan yaduwar cutar korona inda ya gargaɗi mutane cewa bai kamata a rika sakwasakwa da cutar ba.

Ghebreyesus ya ce nau’in Omicron na yaduwa kamar walkiya sannan a yanzu haka asibitoci a duniya sun fara samun daruruwan mutane da ake kai musu kuma har an fara samu karancin jami’an lafiya

Karancin maganin rigakafin cutar korona

Ghebreyesus ya ce karancin maganin rigakafin cutar korona na daga cikin matsalolin dake ci gaba da sa ana rasa mutane, Talauci da durkushewar tattalin arzikin kasashen duniya.

“A makon da ta gabata ne ƙasashen duniya suka fi samu yawan mutanen da suka kamu da korona. Muna kuma da masaniyar cewa akwai mutane da dama da suka kamu da cutar da ba a san da su ba musamman a lokacin hutun kirsimeti da Sabon shekara.

Ya ce karancin maganin rigakafin cutar ya sa wasu kasashe sun fara yi wa mutanen su allurar rigakafin cutar zango na hudu sannan wasu kasashen Basu da isassun maganin rigakafin da za su yi wa jami’an lafiya da wadanda suka fi zama cikin hadari rigakafi har yanzu.

Ghebreyesus ya ce kamata ya yi a haɗa hannu domin ganin an kawar da wannan matsala cewa yin haka ne kawai zai taimaka wajen daƙile yaduwar cutar.

Ya hori mutane da su ci gaba da kiyaye dokokin gujewa kamuwa da cutar tare da yin allurar rigakafin cutar domin dakile yaduwar cutar.

Yaduwar cutar

Alkaluman yaduwar cutar da Worldometer ta fitar na ranar Juma’a ya nuna cewa mutum 301,521,224 ne suka kamu da cutar sannan cutar ta yi ajalin mutum 5,492,798, mutum 38,176,931 na dauke da da cutar a duniya.

An sallami mutum 257,851,495 a duniya.

Zuwa yanzu kasashe 202 sun fara yi wa mutanen su allurar rigakafin korona sannan an yi amfani da kwalaben maganin rigakafin guda 9,315,164,000 a duniya.