TATTAUNAWAR SHUGABAN ƘASA: Batutuwa 10 Da Buhari Ya Bijiro Wa ‘Yan Najeriya Da Su

Tattaunawa biyu da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi da gidan talbijin na Channels da na NTA a ranakun Laraba da Alhamis sun zaburar da ‘yan Najeriya sosai. Yayin da wasu kuma su ka farka daga barci saboda rugugin ƙarar wasu kalaman na Buhari, wasu kuma jijjiga su furucin ya yi. Akwai kuma waɗanda hirar ta zo masu tamkar wani talge ko malmalar tuwo mai zafi.

PREMIUM TIMES HAUSA ta tsakuro 10 daga cikin batutuwan, wanda mai karatu zai riƙa yin tilawar su daga nan har ranar zaɓen shugaban da zai gaji Buhari a 2023.

1. Matasa Su Daina Yin Ilmi Don Kawai Su Yi Aikin Gwamnati:

Shekaru uku bayan Buhari ya kira matasan Najeriya cima-zaune ko ‘yan zaman dankali, a tattaunawar sa da Channels kuma ya ƙalubalance su cewa su daina yin ilmi da nufin su lallai sun yi aikin gwamnati.

Dama kuma a ƙarshen 2021 Buhari ya hore su cewa su tashi tsaye, saboda aikin gwamnatin ma a yanzu ba samuwa ya ke yi ba.

Shugaban na Najeriya ya ce yin ilmi a dawo ana jiran aikin gwamnati, wata tsohuwar al’ada ce tun ta zamanin Turawan mulkin mallaka, inda matashi zai yi ilmi domin ya samu aiki ya mallaki mota, burin sa kenan a rayuwa.

2. MULKIN NAJERIYA: Buhari Ya Ce Ya Yi Bakin Ƙoƙarin Sa:

A cikin tattaunawar sa da NTA, Buhari ya taɓo batun mulkin ƙasa, inda ya ce ya yi bakin ƙoƙarin sa. Sannan kuma ya ce ya na fatan idan za a tuna shi nan gaba bayan saukar sa, to a riƙa tuna shi a matsayin wani gwarzon da ya yi wa Najeriya aiki tuƙuru bakin gwargwadon sa.

Duk da tulin matsalolin da ake fama da su musamman na rashin tsaro, hakan bai hana Buhari cewa ya yi ƙoƙari ba.

3. A Koma Gona Don A Magance Matsalar Tattalin Arziki:

Shugaba Buhari ya amsa zafafan tambayoyin zargin taɓarɓarewar tattalin arziki a zamanin mulkin sa.

A cikin amsar da ya bayar dai ta farko bai, yarda tattalin arzikin Najeriya ya gurgunce a zamanin mulkin sa ba.

Matambaya sun riƙa bijiro masa jadawalin ƙididdigar da cibiyoyi ciki har da Hukumar NBS ta gwamnati ta nuna halin da tattalin arzikin ke ciki. Amma Buhari bai yarda ba.

A ƙarshe amsa ta biyu da ya bayar ita ce a koma gona don harkar noma ce za ta bunƙasa tattalin arzikin Najeriya, ta samar da kuɗaɗen shiga masu yawa.

4. ZAƁEN 2023: APC Za Ta Iya Faɗuwa Zaɓe Idan Ba Ta Tashi Tsaye Ba:

Shugaba Muhammadu Buhari ya ja kunnen jam’iyyar APC cewa idan ba ta yi da gaske ba, to ta na ji ta na gani jam’iyyar PDP za ta karɓe ragamar mulki a 2023, bayan cikar wa’adin mulkin sa.

Buhari na magana ne dangane da rikicin da manyan APC ke fama da shi na neman kasa shirya taron gangamin jam’iyya na ƙasa, domin zaɓen shugabannin jam’iyya.

Da ya ke tattaunawa da gidan talbijin na NTA a ranar Alhamis, Buhari ya yi tsokaci musamman ganin yadda rigima ke neman Kunno kai har taron gangamin na neman gagara.

Baya ga batun shugabancin jam’iyya, babban abin da ya dabaibaye APC shi ne batun ɗan takarar zaɓen shugaban ƙasa, wanda wasu ke neman a cimma yarjejeniyar fidda ɗan takara ba tare da yin zaɓen fidda-gwani ba.

Sai dai kuma Buhari ya ce shi ba shi gwani a cikin dukkan masu tsayawa takara. Don haka abin da doka ta ce a yi wajen fidda-gwani, shi za a yi kawai.

Buhari ya ce ya zama wajibi APC ta tashi tsaye domin bai wa ranar taron gangamin jam’iyya muhimmanci.

“Shi taron gangamin jam’iyya abu ne na wani ƙayyadajjen lokacin da doka ta gindiaya. Kuma tunda mulki bayan shekara huɗu ake canja shi, to ba zai yiwu a ce ba a yi taron gangamin jam’iyya ba a cikin wannan ƙayyadajjen lokacin ba. Saboda idan APC ta yi wasa, sai PDP ko wata jam’iyyar adawa ta karɓe ragamar mulki.

Buhari ya tunatar da yadda wasu gwamnonin da bai ambaci sunayen su ba, ya ce sun same shi da shawarar aikata wani abu da ba daidai ba a kan tsayar da ɗan takara, amma ya ce, “na ƙi yarda, saboda idan na amince, to jefa tsarin dimokraɗiyyar cikin halaka za su yi.”

Daga nan Buhari ya shawarci gwamnoni su bar doka da tsarin dimokraɗiyya su yi abin da ya dace kawai.

6. Canja Sheƙar Ɓarayin Gwamnati Zuwa APC Ba Zai Hana A Ɗaure Su Ba:

A tattaunawar Buhari da NTA, ya yi magana a kan yaƙi da rashawa, inda ya taɓo yadda gwamnatin sa ba ta yi wa hukumomin bincike ko kotu katsalandan.

Daga nan an masa tambihin yadda wasu waɗansu da ake wa zargin wawurar maƙudan kuɗaɗe ke komawa cikin APC, jam’iyya mai mulki.

Buhari ya ce don ɓarawon gwamnati ya koma APC, ai ya gudu, amma fa bai tsira. Ya ce duk mai laifi sai an take ruwan cikin sa ya amayar da abin da ya sata, sannan a ɗaure shi.

6. Matsalar Tsaro: Buhari Ya Ce Ba Kafa ‘Yan Sandan Jihohi Ne Mafita Ba:

Kalaman da Buhari ya yi a tattunawa da Channels kan batun kafa ‘yan sandan jihohi, sun motsa zukatan da dama a Najeriya.

Buhari ya ce ba zai taɓa goyon bayan kafa ‘yan sandan jihohi ba.

Daga cikin dalilan da Buhari ya bayar, har da cewa idan aka kafa, to gwamnonin jihohin ƙasar nan za su yi amfani da su wajen cimma buƙatun su da tirsasa ƙarfa-ƙarfa.

Ya buga misali yadda har yanzu gwamnoni ba su bar wa ƙananan hukumomi ‘yancin su da dokar Najeriya ta mallaka masu.

7. Nnamdi Kanu Ya Ƙwaci Kan Sa A Kotu, Ba Zan Tsoma Baki A Sake Shi Ba:

Buhari ya ce ba zai tsoma baki ya ce a saki Nnamdi Kanu ba, domin yin haka shiga sha’anin aikin kotu ne, wanda ba zai yi ba.

Ya ce an yi wa Kanu adalci, domin kotu aka tura shi inda gaskiyar sa za ta ƙwace shi.

“Mutun ba zai riƙa irin kalaman cin amanar ƙasa da ya riƙa yi ba, sannan a ce ba zai girbi abin da ya shuka ba.” Inji Buhari.

8. Tulin Basussuka: ‘Da Ban Ciwo Bashi Ba, Sai ‘Yan Najeriya Sun Riƙa Tafiya Legas Kasa Daga Ibadan’

Buhari kare tulin bashin da gwamnatin sa ke ciwowa, inda ya ce ai duk ayyuka ake yi da su, ba dacewa a ke yi da su. Dama cikin Oktoba ya ƙalubalanci masu ƙorafi ana ciwo basussuka da yawa.

Ya riƙa buga misali da ayyukan titinan mota da na jiragen ƙasa da ake yi a faɗin ƙasar nan.