KISAN GILLAN ZAMFARA: An tsinci gawarwakin mutane sama da 50 a daidai gogarma Bello Turji zai koma daji da zama

Mazauna kananan hukumomin Anka da Bukkuyum a jihar Zamfara sun bayyana cewa sun tsinci gawarwakin mutane sama da 50 da aka kashe a kauyuka biyar din da ‘yan bindiga suka kona tsakanin daren Talata zuwa Laraban wannan makon.

Mazauna ƙauyukan da ƴan bindigan suka kai wa hari sun ci gaba da neman gawarwakin mutane da na wadanda suka ji rauni.

Wani dan siyasa Hamza Adamu ya bayyana wa wakilin PREMIUM TIMES cewa shugaban kungiyar ‘yan sa kai na karamar hukumar Anka Gambo Abare na cikin adadin yawan mutanen da ‘yan bindigan suka kashe.

“Gambo Abare ya gamu da ajalinsa yayin da shi da abokan aikinsa suka yi arangama da ‘yan bindiga a Kurfar Danya.

“Bani da masaniyar adadin yawan mutanen da aka kashe amma na San da mutuwar Gambo Abare ne saboda shi sananne a wannan yankin.

Ɗaya daga cikin mutanen da suka tsira da rai Murtala Waramu ya bayyana wa VOA Hausa cewa sun kirga gawan mutum 58 daga kauyukan da suka ziyarta.

Waramu ya ce akwai ƙauyuka da dama da ba su shiga ba amma har yanzu akwai gidajen da shagunan dake ci da wuta a ƙauyukan da suka shiga.

Ya ce an tsinci gawarwakin mutum 22 tsakanin wani ƙauye da Kurfar Ɗanya, 8 a Tungar Geza, 6 a Tungar Dan Gayya, 5 a Tungar Toro, 4 a Abare tare da gawan Gambo Abare, 3 a Walo, 2 a Tungar Isa sannan da 1 a Keya.

Waramu ya ce mafi yawan mutanen da aka kashe maza ne magidanta.

Idan ba a manta ba a daren Laraba zuwa safiyar Alhamis ne ƴan bindiga suka kona kauyuka biyar dake kananan hukumomin Anka da Bukkuyum.

Tungar Geza, Rafin Gero, Kurfar Danya, Kewaye da Tungar Na More na daga cikin kauyukan da ‘yan bindigan suka kona.

Turji zai koma daji da zama

Wani da baya so a fadi sunan sa ya bayyana wa VOA Hausa ranar Alhamis cewa sun samu labarin cewa Turji zai koma zama a daji.

“Mun samu labarin cewa an kafa tanti sama da 500 a cikin daji sannan Kona kauyuka biyar din da ‘yan bindiga suka yi yaran Turji ne suka yi yayin da suke wucewa zuwa daji.

Wani Malami dake koyar da darasin tarihi a jami’ar Usmanu Danfodiyo dake jihar Sokoto Murtala Ahmed – Rufai ya bayyana cewa akwai alamun gaskiya a jita-jitan da ake yadawa cewa Turji zai koma daji da zama.

“Su dama Fulani haka suke da yawo sannan na ji cewa dajin da zai koma da zama ya fi dajin Fakai illa.

“Ga dukan alamu Turji zai koma wannan daji ne domin ya kauce wa ruwan bama-baman da rundunar sojin sa ke yi masa lugude.