KORONA: Mutum 9 sun kamu a cikin kwanaki uku a Najeriya

Tun ranar 18 ga Afrilu 2022 da hukumar NCDC ta sanar cewa mutum 22 sun kamu da cutar korona mutum 9 ne suka kamuwa da cutar a cikin kwanaki uku a Najeriya.

Hukumar ta ce an gano wadannan mutane a jihar Legas da Abuja.

Yaduwar cutar

Sakamakon gwajin cutar ya nuna cewa mutum shida sun kamu da cutar a Abuja sannan mutum uku a jihar Legas.

Zuwa yanzu mutum 255,679 sun kamu, an sallami mutum 249,886 sannan cutar ta yi ajalin mutum 3,143.

Har yanzu akwai mutum 2,653 dake dauke da cutar a kasar nan.

Idan ba a manta ba sakataren aiyukka na kwamitin Muktar Muhammed ya ce kwamitin za ta yanke hukuncin game da sassauta dokar amfani da takunkumin fuska bayan an dawo hutun Easter.

Kwamitin ta ce baki da suka shigo Najeriya kuma sun kammala yin allurar rigakafin cutar ba za su yi gwajin cutar ba.

Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya ce baki da suka shigo Najeriya Kuma Basu Yi allurar rigakafin cutar ba ko Kuma ba su kammala yin allurar rigakafin ba za su yi gwajin cutar da zaran sun shigo kasan.

Sai dai bayan kwanaki biyu da fadin haka PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa ana tilasta bakin da suka shigo kasar nan wajen yi da biyan kudin gwajin cutar

Allurar rigakafin korona

Zuwa yanzu gwamnati ta yi wa mutum 33,932,163 gwajin cutar a kasar nan.

Shugaban hukumar NPHCDA Faisal Shu’aib ya tabbatar cewa mutum miliyan 13,588,718 sun kammala yin allurar rigakafin sammqn mutum miliyan 23,012,700 sun yi zango na farko na allurar rigakafin a kasar nan.