Yadda Boko Haram suka kashe mutum 10 a jihar Yobe – Rundunar Ƴan sanda

Rundunar ƴan sandan jihar Yobe ta bayyana cewa mutum 10 sun mutum kuma wasu da dama sun ji rauni a harin da Boko Haram ta kai a garin Geidam ranar Laraba.
Kakakin rundunar Dungus Abdulkarim ya sanar da haka ranar Asabar a garin Damaturu.
Abdulkarim ya ce maharan wanda ke tafiya akan babura sun Kona gidajen malaman makarantar sakandare na gwamnati a Geidam.
“Rundunar ta aika da ma’aikatan ta dake sintiri a garin domin tabbatar da tsaro sannan ta dauki matakan da za su taimaka wajen hana maimaicin haka nan gaba.
Ya ce rundunar na yin qlhinin rasuwar mutanen da Boko Haram suka kai wa hari kuma rundunar ta yi kira ga mutane da su rika taimakawa jami’an tsaro da bayanan sirri da zasu basu daman kaiwa garesu kafin su kai hari.
Idan ba a manta ba a ranar Alhamis PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin harin da Boko Haram suka garin Geidam.
Bisa ga rahotan mutum 12 ne suka rasa rayukansu a wannan harin.
Maharan sun kuma kona gidajen malaman kwalejin koyar da kimiya da fasaha dake garin.
Wani dan sanda da baya so a fadi sunan sa saboda rashin izinin yin magana da manema labarai ya ce maharan sun shigo garin Geidam bayan sun ajiye baburan hawan su a bayan gari.