Kashi 64% na yara kanana basu gama yin rigakafin da ya kamata su yi ba a Najeriya

Sakamakon bincike da aka gudanar ya nuna akalla kashi 64% na yara ‘yan watanni 12 zuwa 23 ba su kammala yin allurar rigakafin su ba a Najeriya.

Sakamakon binciken da MICS da NICS suka gudanar ya nuna yara kanana kashi 46% ba su kammala yin allurar rigakafin su ba daga shekaran 2016 zuwa 2021.

Jami’in UNICEF Claes Johanson ya sanar da haka a taron da ya yi da manema labarai a garin Fatakwal a makon jiya.

Johanson ya ce akalla akwai yara kanana kashi 18% da basu yi allurar rigakafi ba ko da ko sau daya ne.

Ya ce daga shekarar 2016 zuwa 2021 kashi 36% na jarirai ‘yan watanni 12 zuwa 23 ne kadai suka kammala duk allurar rigakafin da ya kamata a yi musu.

Johanson ya ce jihohin Enugu da Ebonyi na daga cikin jihohin da suka dage wajen yi wa yara allurar rigakafi. Jihar Sokoto ce jiha ta baya wajen yi wa yara allurar rigakafi.

A jihar Enugu tana da kashi 1% na yaran da basu kammala yin allurar rigakafi ba, babu ko daya a Ebonyi amma akwai Kashi 51% na yaran da basu kammala yin allurar rigakafi ba a jihar Sokoto.