KASAFIN 2022: Naira tiriliyan 16.39 da Buhari ya gabatar sun yi kaɗan – Babban Daraktan Kasafin Kuɗi

Yayin da Najeriya ke neman inda za ta ciwo bashi domin cike wawakeken giɓin sama da Naira tiriliyan 6, shi kuwa Babban Darakta a Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya, Ben Akabueze, ya bayyana cewa kasafin kuɗin shekarar 2022 ya yi kaɗan matuƙa.

Akabueze wanda shi ne mai jagorantar aikin kasafin Najeriya, ya yi wannan tsinkaye ne a ranar Alhamis, yayin wata hira da aka yi da shi a Gidan Talbijin na Channels.

“Duk da wannan Kasafi na shekarar 2022 shi ne mafi yawan kuɗaɗe a tarihin Najeriya, to gaskiya ya yi kaɗan.

Ranar Alhamis ce Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da Kasafin 2022 a Majalisa, har na Naira tiriliyan 16.39.

Wannan kasafi dai ya hauwa yawan kasafin 2021 da Naira tiriliyan 3.

Buhari ya shaida wa Majalisa cewa an ƙara kasafin ne domin a ƙara wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) Naira biliyan 100 da kuma Naira biliyan 500 da za a amfanar da su wajen inganta rayuwar al’umma.

Haka kuma akwai wata Naira biliyan 50 da Buhari ya ce za a kashe wajen biyan likitoci alawus ɗin saida-rai, sai kuma wasu alawus-alawus da dama

Akabueze ya buga misali da wasu ƙasashen daya ce na su kasafin ya fi na Najeriya sosai. Sannan kuma ya ce tilas Najeriya ke riƙa ciwo bashi idan ana so a riƙa yi wa jama’a ayyukan raya ƙasa.

A kan kasafin 2022, ya ce babu yadda za a yi a aiwatar da wasu ayyukan da ke cikin kasafin sosai idan ba a ciwo bashi daga waje ba.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Sanata Lawan ya damu da wawakeken giɓin da aka samu.

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya nuna damuwar yadda ake ta samun wawakeken giɓi a kasafin Najeriya, musamman na 2022.

Ya yi wannan ƙorafin a ranar Alhamis, lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da Kasafin 2023 a Majalisa.

An dai samu giɓin zunzurutun Naira tiriliyan 6.26, waɗanda Buhari ya ce duk bashi za a rakito domin a cike giɓin.

Lawan ya ce yawan giɓin akwai abin dubawa sosai a ciki, don haka Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya za su bi kasafin filla-filla domin a yi masa aski, sasabe da kwaskwarimar rage wasu kuɗaɗe, ta yadda Najeriya za ta yi kasafin da zai zama daidai ƙarfin aljihun ta, da kuma daidai ƙarfin wuyan da zai iya ɗaukar bashin da za a ciwo.

“Babbar matsalar da ke addabar kasafin kuɗi a Najeriya ita ce matsalar yadda za a karɓi haraji da kuma ta yadda harajin ke shiga aljihun gwamnati.

A lokacin gabatar da kasafin, Buhari ya yi magana kan masu nuna damuwa da yawan bashin da ake ciwowa.

“Duk mai tantamar bashin da mu ke ciwowa ya je kawar da shakku a kan mu.”

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bashin da gwamnatin sa ke ciwowa bai kumbura cikin da zai rikita ƙasar nan ba.

Ya ce ayyukan da ake yi da kudaden da ake ciwowa bashi a bayyane su ke, don haka duk mai tantama zai iya fita ya yi bincike ya gani da kan sa.

Buhari ya yi wannan kalami a gaban gamayyar Sanatoci da Mambobin Majalisar Dattawa, yayin da ya ke gabatar masu da kasafin 2022 na Naira tiriliyan 16.39.

A cikin kasafin dai ya bayyana cewa Naira tiriliyan 4.11 za a kashe su wajen biyan albashi da sauran haƙƙin tafiyar da ma’aikatan gwamnati.

Sai kuma zunzurutun Naira tiriliyan 3.61 waɗanda za su tafi wajen biyan basussukan baya, wanda gwamnati ke yi a kowane ƙarshen wata.

Buhari ya ce za a kashe Naira biliyan 579 wajen biyan haƙƙin ‘yan fansho da biyan garatuti.

Yayin da Buhari ke jawabi, ya yi bitar wasu muhimman ayyukan da gwamnatin sa ta yi a shekarar da ta gabata, sannan kuma ya jinjina wa kan sa bisa ƙoƙarin da ya yi na tsayuwar sama da minti 50 ya na jawabi wajen gabatar da kasafin 2020. Kuma ya ce a wannan ranar ma zai yi bajintar sake yin irin waccan tsayuwar.