Duk da an biya kuɗin fansa, Buzu ya ki sakin mutum 21 da suka sace a Sokoto

Buzu, shine babban mataimakin Bello Turji dake taɓargazar su a jihar Sokoto, na yin garkuwa da mutane, kisa da kuma sace-sace.

Idan ba a manta ba, PREMIUMTIMESHAUSA ta buga labarin yadda ƴan bindiga karkashin Bello Turji suka yi garkuwa da mutane 21 daga Gatawa, Jihar Sokoto.

Buzu wand shine yake tsre da wadannan mutane ya nemi a biya naira miliyan 20 kafin a saki mutanen, kuma ya bada sharaɗin dagacin Katsallen Kade ne zai kawo musu da da kansa.

Mutanen gari sun haɗu sun tara naira miliyan 2.2 amma kuma bayan an kaiwa Turji sai ya amsa ya kuma ki sakin ko da mutum ɗaya ne cikin waɗanda suka yi garkuwa da.

Wani danuwan wata da aka sace ya ce ” mun tara ƴan kuɗaɗen da zamu iya tara wa kuma mun aika wa Buzu amma ya ce dole sai fa an tura masa miliyan 20, ko kuma a hakura da su.