Ƴan shaye-shaye sun cinna wa taragon Jirgin Kasa biyu wuta a jihar Kwara

Wani jami’in hukumar sufurin jiragen saman Najeriya reshen jihar Kwara ya bayyana cewa wasu masu shaye-shaye wiwi da kwayoyi sun babbake taragon jirgin kasa biyu a jihar.

” Waɗannan tarago biyu da suka kona sun saba shigan su suna barankaɗewa da wiwi. Nan ne wurin maskewar su. Bayan sun gama kwalewa ne suka burbudin garwashi da wutar kilan wiwin ya tada gobara a cikin taragon dake manne da juna suka babbake.

Sai dai kuma rundunar ƴan sanda jihar ta bayyana cewa kafin ƴan sanda suna isa wurin gayun sun arce.

Gwamnatin jihar ta ce ba gaskiya bane wai matasa ne suka tare jirgin a lokacin da yake yin lodi daga Legas zuwa Kano, duka tare shi a garin Offa suka cinna musu wuta.

” Waɗannan tarago guda biyu sun daɗe a ajiya ba su aiki.