KARO NA BAKWAI CIKIN WATA HUƊU: ‘Yan bindiga sun banka wa ofishin INEC wuta a Imo, kwana uku bayan babbake wani ofishin

Wasu miyagu ɗauke da muggan makamai sun banka wuta a ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), wanda ke Ƙaramar Hukumar Oru ta Yamma, a jihar Imo.
Sun kai wa ofishin harin banka masa wutar ce a ranar Lahadi ƙarfe 4 na asubahi, kwanaki uku bayan banka wuta a ofishin INEC da ke Ƙaramar Hukumar Orlu, cikin Jihar Imo.
Kakakin Yaɗa Labaran INEC, Festus Okoye ya tabbatar da kai harin, wanda ya ce Kwamishinan Zaɓe na Jihar Imo, Sylvia Uchenna ne ya kai rahoton a Hedikwatar INEC ɗin, a ranar Lahadi.
Okoye ya ce, “an yi asarar kujeru da tebura da wasu kayayyaki, amma ba a ƙone akwatinan zaɓe ba.
A harin da aka ƙone ofishin INEC kwanaki uku baya a Imo, PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa an sake banka wa ofishin INEC wuta, karo na huɗu cikin sati uku.
Wasu mahara sun banka wa ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) wuta a Ƙaramar Hukumar Orlu ta jihar Imo.
Wutar wadda aka banka wa ofishin, ita ce ta huɗu da aka cinna wa ofishin hukumar zaɓe a kudancin ƙasar nan a cikin makonni huɗu.
Kafin wannan hari dai an kai a Ogun, Osun da Ebonyi. Yayin da Ogun da Osun ke yankin Kudu maso Yamma, Ebonyi ta na yankin Kudu maso Gabas.
Kakakin Yaɗa Labaran INEC, Festus Okoye ne ya fitar da sanarwar kai harin a ranar Juma’a.
Ya ce Kwamishinan Zaɓe na Jihar Imo, Farfesa Sylvester Agu ne ya kai wa Hedikwatar INEC rahoton kai wa ofishin na su da ke jihar Imo hari.
Yayin da ba a tantance adadin kayayyakin da aka yi asara ba, Okoye ya ce wani ɓangare na ginin ya lalace.
“Sannan kuma sai da maharan su ka arce da ma’aikatan da ke ƙarasa wani aikin gini a harabar ofishin, har su uku. Amma dai daga baya sun sake su,” inji Okoye.
Ya ce an yi sa’a wutar ba ta yi mumnunan ɓarna ba, domin ‘yan sanda sun isa wurin da gaggawa.
Ba wannan ne karo na biyu da aka kai hari ofishin INEC, bayan wanda aka kai a Ebonyi ba. Cikin watanni huɗu da su ka gabata an banka wuta a ofishin INEC na garin Igbo-Eze ta Arewa, a Jihar Enugu.
Haka nan a cikin watan Mayu an kai wa ofishin INEC hari a Ebonyi, sannan kuma cikin watan Satumba, 2021 an kai wa ofishin INEC na Ƙaramar Hukumar Awgu hari a Jihar Enugu.
Harin baya-bayan nan ya faru ne kwanaki uku bayan da INEC ta yi kira da bada shararwarin cewa idan ana so a magance matsalar kai wa kayan INEC hare-hare, to a riƙa gaggauta hukunta waɗanda aka kama da laifin kai hare-haren.