2023: INEC za ta fara raba Katin Rajistar Zaɓe ran 12 ga Disamba

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za ta fara raba Katin Rajistar Zaɓe (PVC) a ranar Litinin, 12 ga Disamba.
Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran INEC, Festus Okoye ya fitar, ya ce za a ci gaba da aikin raba katin har zuwa ranar Lahadi, 22 ga Janairu, 2023.
Ya ce daga ranar 6 zuwa 15 ga Janairu, 2023, za a koma ana raba mazaɓu 8,809 na faɗin ƙasar nan.
“Amma daga ranar 15 ga Janairu, za a koma rabon katin a ofisoshin INEC da ke ƙananan hukumomi 774 na faɗin ƙasar nan. Za a ci gaba da rabon har a ranar 22 ga Janairu, 2023.”
Okoye ya ce za a fara rabon katin tun daga ƙarfe 9 na safe har zuwa ƙarfe 3 na yamma, a kowace rana, har da ranakun Asabar da Lahadi.
Ya ƙara da cewa Kwamishinonin Zaɓe na jihohi za su gana da masu ruwa da tsaki da su ka haɗa da sarakunan gargajiya da sauran masu riƙe da sarautu, malaman addini, ƙungiyoyi da kafafen yaɗa labarai domin su sanar da su irin tsare-tsaren da za a yi domin tabbatar da an yi rabon katin shaidar rajistar zaɓen a cikin ruwan sanyi, kuma cikin nasara.