KANJAMAU A KOGI: Sama da mutum 43,000 na dauke da cutar a jihar – Zakari

Kwamishinan lafiyar jihar Kogi Zakari Usman ya bayyana cewa mutum 43,373 ne ke dauke da cutar Kanjamau a jihar.

Kwamishinan ya fadi haka a cikinmakon a ranar cutar Kanjamau ta duniya da aka yi a garin Lokoja.

Ya yi kira ga mutane da su daina yada jitajitar cewa babu cutar Kanjamau, wai ba gaskiya bace cutar.

Usman ya kuma ce kamata ya yi mutane su kare kansu daga kamuwa da cutar sannan idan har sun kamu da cutar su nemi magani da wuri.

Ya ce gwamnati za ta ci haba da daukan matakan da za su taimaka wajen rage yaduwar cutar a jihar.

“Gwamnati za ta inganta yin gwajin cutar, karban maganin da wayar da kan mutane kan yadda za su kare kansu daga kamuwa da cutar.

“Sannan gwamnati za ta ci gaba da kokarin wayar da kan mutane game da illar nuna wa masu fama da cutar wariya.

“Gwamnati za ta shigo da dabarun na zamani domin ganin ta inganta yi wa mutane gwajin cutar musamman a yankin karkara.

“Yin gwajin cutar na daga cikin hanyoyin da mutane za su iya sanin ko sun kamu da cutar domin samun maganin cutar.

Ranar 1 ga Disemba ta kowacce shekara ce ranar da aka kebe domin wayar da kan mutane kan da cutar Kanjamau sannan da tunawa da mutanen da cutar ta yi ajalinsu a duniya.