Sojoji sun ceto mutum 4 da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Rundunar sojin Najeriya dake aiki a karkashin ’Operation Forest Sanity’ sun ceto mutum 4 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su inda a cikinsu akwai tsohuwa mai shekara 85 a kananan hukumomin uku dake jihar Kaduna.
Bayan haka sun babbake maboyan ‘yan bindiga dake dazukan kewaye da wadannan kananan hukumomi.
Kwamishinan tsaron jihar Samuel Aruwan ya sanar da haka a garin Kaduna a cikin makon jiya.
Aruwan ya ce dakarun sun ceto mutum biyu da aka yi garkuwa da su bayan sun yi batakashi da ‘yan bindigan a kauyen Kwanti dake karamar hukumar Chikun.
“Maharan sun gudu cikin daji sun bar babura hudu. sannan sun tsinci gawarwakin wasu mata da maharan suka kashe.
Bayan haka Aruwan ya ce ‘yan bindiga sun gudu a lokacin da suka ga zuwan jami’an tsaro a dazukan dake kauyukan Abrom, Gabachuwa da Kujeni dake kananan hukumomin Kajuru, Chikun da Kachia.
Ya ce yayin da dakarun ke rusa maboyar maharan dake dazukan sun kama bindigogi AK-47 biyu da suka lalace, wayoyi uku, rigunan sojoji da kayan hada bam.