Kanawa sun cika da murna bayan dakatar da dandalin Tiwita da gwamnati ta yi a Najeriya

A daidai wasu kungiyoyi da suka hada da SERAP da kungiyar Lauyoyin Kasar nan na kokarin maka gwamnatin Najeriya Kotu saboda abinda suka ce karya doka ce dakatar da shafin tiwita ci gaba da aiki a Najeriya, a Jihar Kano barkewa da murna mutane suka yi game da haka.

Kamfanin dillancin Labaran Najeriya NAN, ta ruwaito cewa mutane da dama da ta zanta da su a jihar bayan sanar da hana Tiwita aiki a Najeriya, sun bayyana jin dadin su matuka game da hakan.

Wasu da dama sun bayyana cewa wannan abu yayi mutukar kyau sai dai ma gwamnati ta bari an dauki lokaci mai tsawo bata dakatar da shafin a Najeriya ba.

” Tiwita tana gina takadararrun mutane ne kawai amma bata da wani amfani a wuri na duk da nima ina bin shafin. Amma Shafin bashi da wani alfanu ga ‘yan Najeriya sai dai ruruta tsiya da rashin kunya kawai.” In ji Usman Kabir

Sakina Habib cewa ta yi ” Duk da ni ma ina amfani da shafin tiwita, amma na yi farincikin dakatar da shafin. Ya zama wuri na ‘yan tasha da masu hankorar tada zaune tsaye a kasa. Sannan kuma daga shugaba Buhari yayi gargadi ga masu son tada husuma a kasa sai su cire wannan gargadi. Hakan da gwamnati ta yi yayi daidai.

Shi ko dalibi Yunusa Abdulkadir, ya ce duk da yana amfani da shafin wajen yin wasu nazarorin karatun sa, zai iya hakura shafin. Shima ya yaba wa gwamnati bisa abinda ta yi.

Ranar Juma’a ne gwamnatin Najeriya ta dakatar da dandalin tiwita dake yanar gizo aiki a Najeriya, saboda ruruta husuma da tashin kankali da take ba wadandu kangararru dama su yi.