Korona ta yi sanadiyar rasuwar wasu ‘yan Najeriya 18 ranar Alhamis

Hukumar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa, NCDC ta bayyana cewa korona ta kashe mutum 18 a ranar Alhamis.

Hukumar ta sanar da haka a shafinta na tiwita.

Zuwa yanzu cutar ta yi ajalin mutum 2, 117 a kasar nan.

Idan ba a manta ba a ranar Litini din da ya gabata hukumar ta bayyana cewa korona ta yi ajalin mutum 28 sannan mutum 203 sun kamu a kasar nan.

Alƙaluman ranar Alhamis sun nuna cewa mutum 122 suka kamu da cutar inda daga ciki jihar Legas na da mutum 105.

Sauran jihohin da aka gano cutar sun hada da Imo-4, Kaduna-4, Akwa Ibom-3, FCT-2, Delta-1, Rivers-1, Oyo-1, Ekiti-1.

Jimlar yawan mutanen da suka kamu da cutar ya kai 166, 682.

An sallami mutum 5, 586 ranar Alhamis sannan jimlar yawan mutanen da suka warke daga cutar zun kai mutum 156, 935.

Jihar Legas

Cikin mutum 105 da suka kamu ranar Alhamis mutum 122 daga ciki duk yan jihar Legas.

Har yanzu jihar ita ce jihar da ta fi yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar nan.

Mutum 59, 057 nes suka kamu a jihar, 439 sun mutu.

An sallami mutum 57,000 bayan sun warke daga cutar.

Har yanzu ana ci gaba da yi wa mutane allurar rigakafin cutar a Najeriya, sai dai kuma a cikin yawan wadnda aka yi musu a kasar, akalla mutum 10,000 sun samu matsaloli daban daban bayan an yi musu rigakafin kafin su girgije.