ZAFTARE MA’AIKATA: Kungiyar Kwadago ta kai karar El-Rufai wajen Buhari kan watsi da yarjeniyar da aka yi da shi a Abuja

Kungiyar Kwadago ta Kasa ta kai karar gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai wajen shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, kan watsi da yarjejeniyar da gwamnatin sa ta yi da Kungiyar Kwadago kan zargin zaftare ma’aikatan jihar.

A cikin wannan wasika da wanda shugaban Kungiyar NLC, Ayuba Wabba ya rubuta wa shugaban Kasa Buhari, ya ce idan ba a ja masa kunne ba kungiyar za ta shiga yajin aiki na duk kasa a dalilin kin bin yarjejeniyar da aka yi da shi.

A wasikar wanda Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya ta wallafa, Wabba, ya kara da cewa gwamnatin Kaduna ta yi watsi da yarjejeyiyar da suka rattaba hannu akai, wanda ya hada da lallai gwamnatin jihar ta dakatar da tsangwamar da ta ke yi wa ma’aikatan jihar da kuma niyyar sallamar da dama daga cikin su.

” El-Rufai ya yi watsi da wannan yarjejeniya da aka saka wa hannu akai a Abuja. Dukka abinda da aka tattauna a zaman da aka yi, babu daya da ya cika. Saboda haka kungiyar ta kai kara fadar shugaban kasa domin idan ba a tilasta masa ya dakatar korar ma’aikata ba za a shiga yajin aiki na duk kasa.

Kungiyar Kwadago ta gudanar da zanga-zanga a Kaduna domin hana gwamnatin jihar karkashin gwamna Nasir El-Rufai, korar dubban ma’aikata da yake shirin yi.

Wannan zanga-zanga yayi munin gaske da ya dakatar da al’amura da dama a jihar.

Sai dai kuma bayan kwanaki uku, kungiyar ta janye yajin aikin bayan saka baki da ma’aikatar kwadago ta Kasa ta yi.

A wannan zama ne da kungiyar ta yi da gwamnatin Kaduna a Abuja a ka saka hannu a wata yarjejeniya wanda NLC ke korafin gwamnatin Kaduna bata cika ba.