TSEREN TSERE WA AREWA A 2022: Shekarar da kasafin Jihar Legas, ya kusa zarce jimlar kasafin Kano, Kaduna, Katsina, Sokoto, Zamfara, Barno, Yobe da Jigawa

Yayin da Arewa ke fama da Boko Haram da kuma ‘yan bindiga, a fannin tattalin arziki da kuma inganta rayuwar al’umma ana ƙara yi wa yankin rata da tazara mai yawan gaske.

Irin yadda matasan Arewa ke ci gaba da yin tururuwa zuwa ci-rani a kudancin Najeriya, hakan na ƙara nuni da cewa tabbas ayyukan bunƙasa rayuwa da kuma matsalolin tsaro na ci gaba da dankwafar da yankin.

Kasafin kuɗin da jihohin Arewa su ka yi na shekarar 2022, ya zama ma’aunin auna irin nauyin koma-bayan da yankin ke ciki, kuma hakan na nufin babu rana, shekara ko lokacin shawo kan lamarin.

Yayin da Jihar Legas ta yi kasafin 2022 na abin da za ta kashe a shekarar har naira tiriliyan 1.758, ita kuwa Jihar Kano da ake wa kallon cibiyar kasuwanci a Arewa, kasafin naira biliyan 196 kacal ta yi. Wato Legas ta nunka Kano kassfi sau takwas kenan.

Abin mamaki shi ne yadda Jihar Katsina ta fi Kano yawan kasafin 2022. Katsina za ta kashe naira biliyan 340.9.

Haka nan Jihar Kaduna ta fi Kano yawan kasafin 2022. Kaduna za ta kashe naira biliyan 278.5.

Jihar Barno inda ake fama da matsalar Boko Haram, ita ma kasafin ta na 2022 ya zarce na Kano. Barno za ta kashe naira biliyan 276. Jihar Zamfara naira biliyan 160, Yobe naira biliyan 164, Jigawa naira biliyan 177, sai Sokoto naira biliyan 188.

Idan aka haɗa kasafin jihohin Kano, Katsina, Kaduna, Barno, Zamfara, Yobe, Jigawa da na Sokoto, za a ga jimla za su kashe kusan daidai da abin da jihar Legas za ta kashe ita kaɗai.

Jimlar kasafin jihohin nan na Arewa su takwas, ya kama naira tiriliyan 1.774.

Babban abin damuwar kuma shi ne, yayin da akasarin kuɗaɗen da waɗannan jihohi na Arewa za su kashe duk daga aljihun gwamnatin tarayya zai fito, ita kuwa Legas yawancin kuɗaɗen na ta daga kuɗaɗen shigar da jihar ke tarawa ne.

Wanann ya nuna jihohin Arewa ba su da wani kataɓus na dogaro da kai, sai dai su dogara da kuɗaɗen fetur da gwamnatin tarayya ke rabawa a kowane ƙarshen wata.