JIHAR NASARAWA: Ƴan sanda sun damke Ɗan’Asabe da ya ci zarafin tsohuwa mai shekaru 80 a Lokonga

Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa ta damke wani magidanci mai suna Dan’asabe Eddo dake da shekaru 45 da ake zargi da cin zarafin wata Gyatuma mai shekaru 80 a kauyen Kundami dake karamar hukumar Lokonga.

Kakakin rundunar yansandan jihar Ramhan Nansel ya sanar da haka ranar Lahadi a garin Lafia a lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Nansel ya ce jami’an tsaro sun samu labarin ta’asar da Eddo ya aikata a kara da aka kawo ofishin ‘yan sanda dake Garaku ranar 14 ga Janairu da karfe 10:30 na dare.

Ya ce Dan’ Asabe Eddo wanda dan asalin jihar Kaduna ne amma yake zaune a kauyen Kundami jihar, Nasarawa ya bi wannan tsohuwa har cikin gidanta sannan ya kule dakinta inda take kwance tana hutawa ya danne ta yayi abinda ya kai shi.

Nansel ya ce Eddo ya tabbatar wa ‘yan sandan cewa shine ya yi wa tsohuwan fyade amma ya roki a yafe masa saboda ya ce ya hudubar shaidan ne ya bi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Adesina Soyemi ya ce fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin haka za ta ci gaba da yin bincike akai sannan bayan haka sai a kaishi kotu domin ya fuskanci shari’a.

Adesina ya hori mutane da su rika sa ido domin kare mutuncin tsoffi daga hannun mutane kamar su Eddo a jihar.