Dalilin da ya sa zaɓen ‘Ƙato a bayan Ƙato’ ba zai yi tasiri a zaɓukan fidda-gwanin-jam’iyya ba – Jega

Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana cewa zai yi wuya a ce zaɓen ‘Ƙato a bayan Ƙato’ na kai-tsaye ya yi tasiri yanzu a zaɓukan fidda-gwani na jam’iyyun siyasa.

Ya bayyana cewa babban dalili shi ne mambobin jam’iyyun siyasa masu ɗimbin yawa ba su ma da rajistar jam’iyyun da su ke goyon baya.

Jega ya yi wannan bayani ne a wurin taron ganawa kan makomar Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe, taron da ƙungiyar Yiaga ta shirya ranar Lahadi a Abuja.

Maƙasudin taron dai shi ne domin a yi kira ga Majalisar Tarayya ta gaggauta miƙa ƙudirin, sannan kuma a magance tankiya da kiki-kakar da ke cikin ƙudirin.

A cikin ƙudirin dai wanda Majalisar Dattawa ta miƙa a cikin 2021, Doka mai Lamba 87 ta bai wa jam’iyyun siyasa damar yin amfani da tsarin zaɓen kai-tsaye na game-gari kaɗai domin fidda gwanin takarar jam’iyyu.

Sai dai kuma cikin watan Disamba Shugaba Buhari ya yi fatali da ƙudirin ta hanyar ƙin sa masa hannu ya zama doka, bisa hujja ko dalilin cewa zaɓen game-gari wajen fidda ‘yan takara zai ci maƙudan kuɗaɗe masu yawa, kuma za a danne wa jama’a haƙƙin su.

Sai dai kuma a wata tattaunawa da aka yi da Buhari kwanan nan, ya ce idan Majalisa ta gyara ƙudirin ta saka amincewa da ɗan takarar da yarjejeniya ta fitar ba tare da zaɓe ba, kuma ta saka cewa a ci gaba da zaɓen ɗan takara bisa tsarin wakilan jam’iyya, wato ‘delegates’, to zai sa wa ƙudirin hannu.

Haka shi ma Jega ya ce ya yi amanna zaɓen game-gari ba shi ne mafita wajen fidda ɗan takara ba a irin yanayin da Najeriya ta ke ciki a yanzu.

Ya ce tabbas ƙasar nan ta na buƙatar sabbin dokokin zaɓe kafin 2023, amma kuma zaɓen fidda-gwani ta hanyar zaɓen game-gari, ba hikima ko dabara ba ce, saboda a cewar Jega tsarin ciki ya ke da miskiloli.

“Tabbas ana ta cewa gwamnoni ne ke yin yadda su ke so wajen zaɓen fidda gwani. To an ji, amma kuma jam’iyya nawa ce ke da cikakkun halastattun mambobi masu rajista?”