JIGAWA: Matasa sun lakadawa shugaban jam’iyyar APC dukan tsiya, yanzu yana kwance a asibiti

Shugaban Jam’iyyar APC na karamar hukumar Dutse a Jihar Jigawa, Yakubu Ibrahim, ya sha duka a hannun matasa ‘yan Jam’iyya saboda zarginsa da cin amanar Jam’iyya.

Hakan ya faru ne jim kadan bayan gwamnan jihar Muhammad Badaru ya bayyana sunayen ‘yan takara na kujerun ciyamomi na kananan hukumumi a jihar.

Maitaimakawa gwamna Badaru kan harkar yada labarai, Auwal Sankara, ya bayyana Bala Chamo, a matsayin dan takarar shugabancin karamar hukumar Dutse.

Hakanne ya harzuka matasan da zargin shugaban jam’iyar na kulla makarkashiya wajen zaben Chamo wanda suka ce bai daceba saboda bashi da farin jinin cin zabe.

Matasan sun lakada masa dukan ne a lokacin da ake tsaka da taron masu ruwa da saki a ofishin jam’iya na karamar hukumar Dutse, dake babban birnin Jihar ta Jigawa.

Shugaban jam’iyar mai shekaru 70 an kwantar dashi a asibiti sanadiyar faruwar hakan.

Kwamishinan yan sanda na Jihar Jigawa, Usman Gomna ya shaidawa manema labarai cewa hakan ya faru amma ba’a sace shi ba kamar yadda wasu ke yadawa.

Kwamishinan yace rigima ce kawai ta cikin gida, kuma ‘yan sanda sun shiga sun kawar da fitinar harma da kama mutum hudu.

Kwamishinan ‘yan sanda ya ce matasan sun dauke shugaban jam’iyyar ne cak daga wurin taron, suka sika kai shi wani wuri dabam, sannan suka ci gaba da sirfar shi bayan wanda suka yi masa a wurin taron.

Ya ce ba gaskiya bane watsawa da ake yi wai sace shi aka yi.